‘Yar Ganduje ta kammala karatu a Kwalejin King’s da ke Landon

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi murnar kammala karatun ‘yarsa Fatima a Kwalejin King’s da ke Landon.

Rahotanni sun bayyana cewa, Fatima ta kammala karatun digiri na biyu, wato digirin digir a King’s College London da ke Birtaniya.

Tsohon gwamnan ya wallafa hakan a wani bidiyo da ke nuna shi cikin farin ciki yana rungumar ‘yarsa sanye da rigar kammala karatu, kafin ya miƙa mata furanni domin taya ta murna.

A cikin sakon da ya rubuta tare da bidiyon, Ganduje ya yaba wa Fatima bisa jajircewarta, ladabi da kuma ƙarfi hali, tare da yi mata fatan alheri a sabon matakin rayuwarta.

​Fatima, wadda matar Idris Ajimobi ce, wato ɗan marigayi tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, ta kammala karatun nata ne a ranar Alhamis daga kwalejin.

By Babaji