Jigawa: Ta yi ajalin mijinta da maganin ɓera don ba ta son shi

Spread the love

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Jigawa, ta tabbatar da kama wata amarya bisa zargin kashe angonta makoni bayan aurensu.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Lawal Shi’isu Adama ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Guaza da ke yankin Ƙaramar Hukumar Jahun, bayan da aka zargi matar da amfani a shinkafar ɓera (guba) wajen kashe mijin nata.

Bayanan farko da ‘yan sanda suka samu sun nuna cewa angon ya ci abincinsa na rana a gida daga nan ya fara jinya, lamarin da ya a aka gaggauta kai shi asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

”Bayan da aka kama wadda ake zargin ta tabbatar wa ‘yan sanda cewa ita ce ta sa masa gubar a abincinsa, bayan da ta aiki wani ɗan’uwanta ya sayo mata shi a kasuwa”, inji sanarwar.

Amaryar ta ce iyayenta ne suka yi mata auren dole ne da mutumin da ta ce ba ta so, abin da ta ce ya sa ta ɗauki matakin kashe shi.

Tuni dai kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin faɗaɗa bincike kafin gabatar da ita a gaban kotu.

Ba wannan ne karon farko da ake samun matsalar kisa tsakanin ma’aurata ba a Nijeriya, wanda galibi ya kan faru sanadiyyar auren dole ko saɓani da abokin zama.

By Babaji