Shettima ya koma Abuja daga taron tattali a Switzerland

Spread the love

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya koma Abuja bayan balaguron da ya yi inda ya shafe mako guda yana gudanar da harkokin difulomasiyya da tattalin arziƙi a ƙasashen Guinea-Conakry da Switzerland.

Wata sanarwa da mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha ya fitar, ta ce mataimakin shugaban ƙasar ya isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe ranar Asabar.

Shettima ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a wajen bikin rantsar da shugaban ƙasar Guinea, Mamadi Doumbouya, ya kuma jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron tattalin arziki na duniya (WEF) karo na 56 a Davos.

Da farko dai Shettima ya ziyarci birnin Conakry, inda ya halarci bikin rantsar da shugaba Doumbouya, inda ya jaddada rawar da Najeriya ke takawa a cikin ƙungiyar ECOWAS da kuma buɗe sabbin hanyoyin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu a fannin noma da masana’antu.

A cewar mataimakin shugaban ƙasar, wannan tafiya ta nuna yadda gwamnatin Najeriya ta ƙara ƙaimi wurin tabbatar da haɗin kan yankin yammacin Afirka da kuma ƙudurin da ta ɗauka na sake farfado da tattalin arzikin ƙasa ƙarƙashin shugaba Tinubu.

By Babaji