Matsalar tsaro: Nijeriya ta samar da runduna ta musamman da ba su horo daidai da zamani

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan tsaron Nijeriya, Muhammad Badaru, a ranar Litinin ya ƙaddamar da rukunin farko na horas da runduna ta musamman mai dakaru 800 kan wani atisayen na musamman.

Badaru a yayin da yaƙe ƙaddamar da shirin horas da rundunar sojin Nijeriya a barikin soji na Kabala da ke Jaji a jihar Kaduna, ya ce, runduna za ta mai da hankali ne wajen kai ɗauki da ofureshan na gaggawa.

Sannan ya ƙara da cewa wannan shiri wani ɓangare ne na sabbin dabarun magance daɗaɗɗen rashin tsaro da ƙasar nan ke fama da shi.

Ya bayyana cewa la’akari da irin yadda sabbin ƙalubalen tsaro ke daɗa ɓullowa, akwai buƙatar samar da runduna ta musamman da za ta samu horo mai kyau da kayan aiki na zamani.

Kuma babbar manufar ita ce samar da ƙwararrun jami’ai masu karsashi da shirin ko-ta-kwana da za su iya kai samame na musamman a wurare masu wuyar gaske.

“Horaswa ta musamman da za a ba wa rundunar an tsara ta ne domin bai wa jami’an sojin ƙwarewa da dabarun yaƙi da ta’addanci da tattara bayanan sirri da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.”

“La’kari da irin sauyin da ake da shi na ƙalubalen tsaro a ƙasar nan, wannan horaswa za ta ƙara samar da haɗin kai a tsakanin jami’an rundunar sojin Nijeriya da rundunar sojin ruwa da rundunar sojin sama da sauran jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukansu,” in ji ministan.

“Za a tura sabbin jami’an tsaron ne zuwa wuraren da ke fama da matsalar tsaro matuƙa,” inji Badaru.

Sannan ya ce jami’an 800 su ne rukunin farko na jami’ai 2,400 da aka tsara bai wa horaswa a matsayin dabara mai dogon zango ta samar da dakarun da za su iya yin gogayya da sauran ‘yan uwansu na duniya da ɗaga matsayin rundunar sojin Nijeriya.

Daga nan ne ya buƙace su da su ɗaura ɗamarar wajen nuna tsage damtse da himma wajen gudanar da ayyukansu da rungumar ɗaga darajarsu da aka yi a matsayin dakaru na musamman.

Ya kuma yaba wa shugaban ƙasa, Bola Tinubu, saboda irin ƙoƙarinsa na tallafa zuba jari ga harkar tsaro ta hanyar samar da kayan soji na zamani da inganta walwalar jami’an rundunar.

A yayin da yake jawabi, babban hafsan sojin Nijeriya, Christopher Musa, ya ce wannan horaswa na da muhimmancin gaske ga tarihin rundunar sojin Nijeriya saboda zai buƙasa irin himmar jami’an da tsaron ƙasa ta hanyar kayan aiki da ake ya yi da kuma bai wa jami’an ƙwarewar da suka buƙata.

Ya ce tsarin yaƙin da ake a yanzu ya nuna akwai buƙatar bai wa jami’an sojin horaswa da kayan aiki da za su iya fuskantar kowanne irin ƙalubalen tsaro cikin sauri da sanin abin da ya kamata da yin aiki bisa gogewa.

Shi ma ya gode wa gwamnatin tarayya yana mai cewa wannan shiri zai tabbatar da salon jagorancinsa na “rainon ƙwararrun jami’an sojin Nijeriya da za su mai da hankali ga hidimta wa al’umma da iya sauke nauyin da aka ɗora musu da iya haɗa kai a kowanne hali.

Shi ma gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce wannan horo na nua irin yadda Nijeriya ta himmatu wajen inganta tsaro da ƙarfafa tsarin tsaro wajen yaƙi da duk wata barazana da za ta tunƙaro Nijeriya.

Gwamnan ya samu wakilcin mataimakiyarsa Hadiza Balarabe, wacce ta ce gwamnan ya ce, la’akari da irin yanayin al’ummarmu, ana cigaba da samun barazanar tsaro kamar na ta’addanci da ‘yan bindiga, ga matsalar masu kutse ta intanet da laifuka na ƙasa-da ƙasa da makamantansu.

“Domin magance wannan matsala, akwai buƙatar rundunar sojin Nijeriya su samu horaswa mai kyau gaske da dabarun atisaye na musamman da samun ƙarfin guiwar da ya kamata domin yaƙi da waɗannan ƙalubale.”

“Wannan horaswa ta musamman wani babban mataki ne samar da wata runduna ta musamman da za ta iya kare ƙasar nan da irin gogewa da tattara bayanan sirrin da ake buƙata wajen tunkarar kowacce irin matsala.”

Sannan gwamnan ya ce, wannan yanayi da Nijeriya ta samu kanta a ciki ya tilasta mata ƙirƙirar hanyoyi da bayar da horo da ƙwarewa wanda zai ba su damar baya ga tunkarar makiya a filin daga har ma da ɗaukar mataki a wani yanayi mai wahalar gaske.

By ukarofi