Matsalar warin baki da hanyoyin magance ta

Daga BILKISU YUSUF ALI

Babbar matsalar da takan haifar da rashin jituwa da tsana da damuwa ga ma’aurata wadda wannan matsalar wata babbar damuwa ce in ta ta’azzara tana iya raba aure ko kai tsaye ko a kaikaice an sani ko ba a sani ba.

Wannan za mu tattauna a yau wadda matsala ce da take ci wa ma’aurata tuwo a kwarya wannan matsala kuwa ita ce matsalar warin baki. Baki a zamantakewar aure yana da muhimmanci kwarai da gaske don yana cikin ‘yan aike da ke fara isa don nuna ƙauna da tayar da sha’awa da ɗaukar hankali. Duk kuwa lokacin da ya kasance abokin zama yana da matsala ta warin baki to an kasha wannan gaɓar ta isar da saƙo.

Duk inda mutum ya kai ga kwalliya da kyau da tsafta idan har yana magana ana jin warin bakinsa to tabbas an samu matsala. Warin baki na kunyata mutum musamman ma’aurata yayin magana ko mu’amala ta kusantar juna wanda in ya zama dole to sai ana yi ana kawar da kai yayin magana.

Dalilan da kan haifar da warin baki:
Matsaloli da daman gaske kan haifar da fitar iska mai wari daga baki daga ciki akwai:-
Rashin kula da tsaftar baki. Ko dai rashin wankewa ko kuma a ci abinci ba tare da ko kuskure baki ba a kwanta a haka ko barin datti a tsakanin haƙori ko dasashi.
Babbar illar da kan haifar da warin baki akwai shaye-shaye. Shan sigari da nau’ikanta kamar wiwi da giya da sauransu
Rashin gudanar yawu a cikin baki.
Bushewar baki
Cutar daji ko hanta.
Kwayoyin cuta na bakteriya
Ɗaukar dogon lokaci ba tare da an sa abu a baki ba. Wato ƙaurace wa abinci
Ciwon sanyi in ya yi yawa a jikin mutum yana haifar da warin baki.
Haka in warin baki ya yi ƙamari za a ga wani abu fari-fari a kan harshe.
Abin lura dai anan in har mutum yana fama da warin baki a cikin ma’aurata mace ko namiji yana da kyau ya nemi magani don gudun cusgunawa abokin zamansa. Shi larurar warin baki tana naso ne a zamantakewa ta kan zama kalanzir don tana rura rigima ko ɗan laifi kaɗan sai a fake da wannan laifin amma a can ƙarƙashin ƙasa ba wannan ne ainihin laifin ba laifin shi ne wannan warin da ke fita daga baki ne wanda ke haifar da rashin nutsuwa yayin kusantar juna.

Ga mai neman ƙarin bayani ya turo saƙon tes a wannan layin ko ta whatsup 08039475191 ko a duba facebook page ɗina Ilham special care and treatment.