Yadda bajekolin littafai da al’adun Hausa na duniya ya gudana a Kaduna

Daga IBRAHIM HAMISU a Kaduna

A ranar Alhamis ɗin makon jiya ne aka gudanar da babban taro mai suna ‘Hausa Internation Book and Arts Festival’ wato bikin bajekolin Littafai da al’adun Hausa na duniya.

Bikin bajekolin littafai da al’adun Hausawa na duniya da ya gudana a Arewa Hausa da ke birnin Kaduna, taken taron dai shi ne Sarari wato (spaces).

Taron wanda aka yi kwana uku ana gabatar da shi, an kuma fara ne a Ranar Alhamis inda aka fara da Hausa da Hausawa a doron ƙasa wanda Farfesa Abdullah Uba Adamu da Farfesa Ibrahim Malumfashi suka gabatar, wanda suka tattauna akan asalin Hausa da Hausawa, haka kuma Farfesa ya tabbatar da da cewa babu gidan Bahaushe yanzu a Ƙasar Hausa, saboda shi Bahaushe ba ya yin kusurwa a gininsa yana yi ne a kewaye.

“Duk gidan da ka je ka ga soro ba za ka ce gidan Bahaushe ba ne, saboda bahaushe bai san soro ba, bai san Azara ba bai san bene ba, bai san Tubali ba, amma ka ga yanzu ana yin su” In ji Farfesa Abdullah.

Shi ma a nasa ɓangaren Farfesa Ibrahim Malumfashi wanda shi ne ya jagoranci matasan da suka shirya taron, ya yaba masu sannan ya jinjina masu inda ya ce dukkanninsu matasa ne da shekarun bai kai kai 30 ba, sannan ya godewa waɗanda suka tallafa taron ya gabata irin Bristol University da sauran ƙungiyoyin da suka tallafa.

Sannan aka ta fi tattaunawa ta biyu mai taken: ‘Magada ‘yan Mazan jiya a harkar Rubutun Hausa’ inda aka tattauna da Salim Yunusa, Maryam Sokoto, Fatima Hussain El-Ladan, sai Khalid Imam ya jagorancesu.

Sai tattaunawa ta uku Mai taken ‘Waƙa daga bakin mai ita’ inda aka tattauna da Malam Yahaya Makaho wanda Muhammad Malumfashi ya jagoranci yin hira da shi.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci ne dai sai tattaunawar ta koma da harshen Turanci mai taken ‘Art Management & Literary activism in North an Nigeria’ inda shugabannin ƙungiyoyin Hiltop creative Arts, Open Arts, Poetic Wednesday, Ayamba LitCast suka gabatar. Dr. Dima Chami ta jagoranci tattaunawar.

Sai aka shiga tattaunawa ta biyu da Ingilishi inda aka yi tattaunawar ‘Ga-ni- ga-ka’ wato Zoom mai taken ‘Gender, Narrative & Hausa Literature’ wanda Dr. Umma Aliyu da Prof. Asabe Kabir suka gabatar, Dr. Carmen McCain ta Jagoranta. 

Sai aka shiga tattaunawa ta bakwai inda aka tattaunawa akan: Sabon salon waƙa da wasan kwaikwayo a Arewacin Nigeriya inda aka tattauna da Sani Liyaliya mawaƙi da Maryam Abubakar Abdullahi ‘yar Fim wanda Bilkisu Yusuf Ali ta jagoranta. Yayin da daddare aka kalli Fim ɗin Shehu Umar na Hausa.

Taron na shiga rana ta biyu wato Juma’a inda aka shiga tattaunawa mai taken: ‘Ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne’ wanda Halima Ahmad Matazu da Dakta Aliyah Adamu suka gabatar, Dr. Halima Daura ta jagoranta.

An shiga tattaunawa ta biyu a ranar Jama’a inda aka tattauna aka batu mai taken ‘Labarin Hausa a Rubuce 1927- 2021’ inda aka tattauna da Ado Ahmad Gidan Dabino MON da Balarabe Ramat Yakubu wanda Dakta Bashir Abusabe ya jagoranta.

Bayan dawowa daga sallar Juma’a ne a ka cigaba da tattaunawa da Dakta Aliya Adamu da kuma Farfesa Ibrahim Malumfashi, wanda Hassana Maina ta jagoranta.

Daga nan aka cigaba da tattaunawa da harshen turanci mai taken ‘Booklogue (Hausa) waiting Northern Nigeria in English’ Wanda Abubakar Adam Ibrahim, Rechard Ali, da kuma Hadiza Isma El-rufai suka tattauna akai, Fauziyya ta jagoranta. Sannan aka kalli shirin sinima mai taken ‘Ina Dadiyata?’

Kazalika, an tattauna akan matsalar tsaro mai taken: Matsalar tsaro a Arewa Ina aka kwana Hassana Maina, Sulaiman Usman Yusuf, da kuma kwamishinan tsaro na Jihar Kaduna Samuel Aruwan, wanda Hamza Ibrahim Baba ya jagoranta.

A zantawarsa da Manema labarai Dakta Bashir Abusabe na Jami’ar Ummaru Musa ‘yaradu’a ya ce, wannan babban taro ya zo akan gaɓa, domin rubutu na Hausa rubutun ƙagaggun labarai sun riga sun shiga zukatan al’ummar Hausawa, saboda haka babu yadda za ka yi ka kankaresu daga rayuwar Hausawa, to kunga kenan wannan taro da aka yi na tattauna matsaloli da ake samu ta fuskar marubutan ta fuskar manazarta ta fuskar abin da ake samu kuma ake ji ana gani daga rubutan, da kuma tasirin da ya je da shi.

“To ka ga kenan taron yana da muhimmanci domin ya daidaita wannan tunanin na marubuta da kuma makaranta ko masu sauraro,” inji Dr. Abusabe.

An ƙarƙare taron da waƙoƙin Hausa na Hausa da na Turanci kamar su Farfesan waƙa, Aminu Ladan, Abuwake, Bilkisu Tambuwal, Sadir Mato da Abdulbasit da sauransu.

Taron ya ƙarƙare da bita da aka yi wa marubuta Hausa da suka zo daga sassa daban-daban da ke faɗin ƙasar nan.