INEC ta shirya wa zaɓen gwamnan Anambra na ranar Asabar – Yakubu

Daga WAKILINMU

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Anambra cikin lumana wanda za a yi a ranar Asabar mai zuwa, 6 ga Nuwamba.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a yayin da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Talata a ofishin hukumar da ke garin Awka, babban birnin jihar.

Ya ce: “Lokacin da hukumar ta saki jadawalin ranakun da za a gudanar da zaɓen, watanni bakwai da su ka gabata, tunanin da wasu su ka yi shi ne lokacin ba zai zo ba.

“To ga shi har lokacin ya zo, saura kwana huɗu kacal su ka rage mana, kuma za mu ci gaba a hakan a matsayin mu na hukuma.”

Yakubu ya ce hukumar ta shirya domin gudanar da zaɓe fisabillahi, kuma mai adalci da inganci.

Ya yi la’akari da cewa ƙalubale guda ɗaya kacal da hukumar ke fuskanta shi ne yadda za ta tabbatar da cewa sababbin masu zaɓe da aka yi wa rajista sun shiga zaɓen an yi tare da su.

Ya ce, “Don tabbatar da cewa sababbin masu zaɓe da aka yi wa rajista su ma sun yi zaɓe, mun yanke shawarar mu tuntuɓe su ta hanyar imel ɗin su da lambobin wayar hannun su domin mu sanar da su wuraren da za su je su karɓi katittikan su.”

Shugaban, wanda ya ce ya kai ziyara jihar ne domin ya yi jawabi ga taron da za a yi da masu ruwa da tsaki a zaɓen a ranar Laraba, ya ce taron zai ƙunshi rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin ‘yan takarar zaɓen.

Ya yi kira ga dukkan masu zaɓe da su fito a yi zaɓen da su tunda an yi duk wani shiri na tabbatar da gudanar da zaɓen a cikin lumana.

A nasa tsokacin, Kwamishinan ‘Yansanda na jihar, Mista Echeng Echeng, ya ce su ma hukumomin tsaro sun gama duk wani shiri domin zaɓen.

Echeng ya ce akwai isassun ababen hawa, kwale-kwale da helikwaftoci da za a yi amfani da su wajen sa ido a dukkan faɗin jihar.

Ya ƙara da cewa sauran hukumomi ma sun gama nasu shirin.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro za su taƙaita zirga-zirgar jama’a daga tsakar daren ranar Juma’a, 5 ga Nuwamba, don hana shigowar ɓatagari zuwa cikin jihar.