Ni ce mace ta farko da aka fara ba wa shugabar jam’iya a Katsina – Mariya Abdullahi

“Na yi tafiye-tafiya da Obasanjo don neman a yafe wa Nijeriya bashin da ake bin ta”

Daga UMAR GARBA, a Katsina

Hajiya Mariya Abdullahi gogaggiyar ma’aikaciyar gwamnati ce wadda ta yi aiki a ma’aikatu daban-daban kama daga Jihar Katsina, sauran jihohin ƙasar nan da ma ƙasashen ƙetare, ta kuma kasance shahararriyar ‘yar siyasa da ta yi takara kuma ta samu nasarar zama shugabar ƙaramar hukuma, mai bai wa tsohon Shugaban Ƙasa Umaru Musa Yar’adua shawara ta musamman, kwamishiniyar yaɗa Labarai, ta kuma taɓa kasancewa mamba a majalisar wakilan Tarayyar Nijeriya. Manhaja ta tattauna da Hajiya Mariya Abdullahi akan batutuwan da suka haɗa da aikin gwamnati, siyasa, abubuwan da suka shafi mata da kuma ƙalubale da nasarori da ta samu a rayuwarta:

Hajiya masu karatu za su so su ji taƙaitaccen tarihinki?
Sunana Hajiya Mariya Abdullahi wasu kuma na kira na da Honourable Mariya Abdullahi. An haife ni a garin Bakori kimanin shekara sittin da wani abu da ya wuce, na yi Makarantar ‘Primary’ a St.Barths Boarding school Wusasa dake Zaria a shekarar 1960, na fara Makarantar ‘Secondary’ a Queens College da ke Kaduna amma ban kammala ba a can saboda wani dalili daga baya sai na koma Saints Maria Goretti dake Benin City a nan ne na kammala karatun ‘secondary’ a 1971, daga nan sai na tafi Ƙasar England inda na yi karatun Diploma a Makarantar ‘London School of television production’ bayan na gama sai na dawo gida Nijeriya inda na yi karatun Digiri na a jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa dake Bauchi a kan ‘Business Management’.

Na fara aiki tun lokacin da na kammala karatun sakandare, ko da yake tun mu na sakandare akan kira mu a gidan Radiyon Kaduna don mu gabatar da wasan kwaikwayo da ‘yan waƙe-waƙe na ‘yan makaranta. Na yi aikin jarida na kuma wakilci ƙaramar hukuma ta a majalisar wakilai ta tarayya, na kuma zama zaɓaɓɓar shugabar ƙaramar Hukumar Bakori, na yi kwammishiniyar yaɗa labarai da al’adu. Bayan nan na zama mai bawa tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua shawara akan harkokin mata a lokacin ya na gwamnan Jihar Katsina.

Waɗanne aikace-aikace ki ka fara kafin ki shiga siyasa?
Kafin in shiga siyasa mafi yawan aikace-aikacen da na yi shine aikin jarida, na fara aiki a gidan Radiyo Nigeria Kaduna a matsayin ‘Announcer’ wato mai gabatar da shirye shirye duk da cewa babana ya so in yi aikin asibiti to Allah dai bai nufa ba, sai na fara aiki a gidan Radio da talabijin dake Kaduna, mu na aiki kuma ana ƙara ba mu horon sanin makamar aiki kamar yadda zaka gabatar da shirye shirye haɗa shiri da kuma tacewa gami da fassara daga Turanci zuwa Hausa.

An tura ni don inyi kwasa-kwasai a wasu jihohin Nijeriya kamar Lagos da kuma ƙasashen waje don mu ƙara gogewa a kan aikin mu. Bayan gabatar da shirye shirye irin su ‘don iyalanku’ da shirye shiryen kiyon lafiya da sauran su bayan na kwashe kimanin shekara 16 ina aikin jarida sai mutanen ƙaramar hukumata wato Bakori su ka shawarce ni da cewar ya kamata in shiga siyasa, da dai ban karɓi kiran da su ka yi mani ba amma daga baya sai aka sanar da maigidana shugaban gidan talabijin na Jihar Katsina to shima dai ya ƙarfafa mani gwiwa akan in shiga siyasa daga baya dai na karɓi kiran su na shiga harkar siyasa.

Bayan kin shiga siyasa, wacce kujera ki ka fara yin takara akai?
To, kujerar da na fara yin takara ita ce kujerar shugabar ƙaramar hukuma a shekarar 1990 a jam’iyar SDP kuma Allah ya ba ni nasara na ci zaɓe, na kuma yi takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya a 1992 a wajajen shekarar 1993 bayan shugaban ƙasa Abacha ya rushe dukkan jam’iyyun siyasa sai na dawo gida Jihar Katsina inda aka bani muƙamin babbar darakta a ma’aikatar Kasuwanci da masana’antu a 1994.

Bayan nan sai aka mai da ni ma’aikatar mata a matsayin babbar sakatariyar ma’aikatar, daga nan sai aka samu canjin gwamnati aka koma mulkin dimokaraɗiyya, bayan an kafa jam’iyar PDP sai ya kasance ni ce mace ta farko da aka fara ba wa muƙamin shugabar matar jam’iya a Katsina amma ban daɗe ba akan kujerar sai aka yi zaɓe inda aka zaɓi marigayi Umaru Musa Yar’adua wanda shi ne ya bani kwamishinar ma’aikatar yaɗa Labarai da al’adu, daga nan sai Umaru Musa ya yi garambawul a majalisar kwamishinoninsa sai kuma ya mai da ni a ma’aikatar jin daɗi da walwala da raya karkara da kuma kula da ci gaban matasa da wasanni, wannan duk ma’aikata ɗaya ce nake gaya maka da aka bani na yi shugabancinta.

Bayan ‘Yar’adua ya gama mulkinsa na farko, ko da ya sake cin zaɓe karo na biyu sai kuma ya bani mataimakiya ta musamman mai ba shi shawara akan harkokin mata muƙamin da na riƙe har lokacin da ya zama shugaban ƙasa.

An kuma zaɓe ni a matsayin mamba a cibiyar dake bunƙasa ci gaban mata ta ƙasa, na kasance cikin Kwamitin amintattu na Hukumomi daban-daban a ƙasar nan, na kuma zama mamba a Kwamitin dake kula da harkokin ƙasashen waje. Na kuma yi aiki da UNICEP ta majalisar Ɗinkin Duniya inda aka zaɓe ni wadda za ta jagoranci fitattun mata goma da suka fito daga jihohin Katsina, Neje, Bauchi, Zamfara da Sokoto a ƙarƙashin wata ƙungiya da ake kira HILWA.

HILWA ƙungiya ce da aka kafa wadda take ɗaukar nauyin karatun mata daga ‘primary’ zuwa ‘secondary’ har zuwa jamai’a, tana kuma taimakawa don bunƙasa ilimin mata don a samu mata malaman Makaranta, mata likitoci, mata lauyoyi da sauran ɓangaren aikace-aikace a jihohin da na faɗa maka.

Wacce rawa ki ke takawa ta fannin siyasa a halin yanzu?
Idan aka ce mutum ya riƙe muq’ƙaman siyasa daban daban kuma ya yi fice kamar ni to da wahala a raba shi da harkar siyasa bakiɗaya, saboda akwai muhimman abubuwa da suke tasowa waɗanda sai an koma an nemi shawarar ƙwararru don haka ne ya sa har yanzu ina taka rawa ta fannin siyasa saboda koda ka nemi ka koma gefe sai wasu sun nemo ka koda da bada shawara ne ko kuma bada wata gudummawa.

Ta wace hanya ki ke ganin gwamnatoci za su taimakawa mata don su cimma burin su na rayuwa?
Akwai hanyoyin da yawa, na farko a ƙarfafa ma mata gwiwa kamar ni dukkan abunda zan yi to zan yi shi iyakar iyawata, na biyu gwamnatoci su ci gaba da ba ilimin mata muhimmanci saboda idan baka da ilimi ba lallai bane ka iya cimma burinka na rayuwa. Bayan nan mata na buƙatar a tallafa ma su ta ɓangarori daban-daban.

Ki na da burin sake neman wata kujerar siyasa a nan gaba?
Ba na zaton sake neman wata kujerar siyasa saboda muƙaman da na riƙe a ma’akatu daban-daban da kuma na siyasa sai dai in ce alhamdu lillah duk wanda ya sanni zai yi tunanin na tara miliyoyin kuɗi wanda ba haka bane sai dai na tara lambobin yabo koda a cikar Nijeriya shekara 50 da samun ‘yancin kai ina cikin waɗanda aka ba lambar yabo ta ƙasa.

Waɗanne ƙasashe aiki ya kai ki?
Na je ƙasashen duniya daban-daban irin su Amurka, England (Burtaniya), Indiya, Japan, China, Saudi Arabia, Senegal, Togo da sauran su a dukkan ƙasashen nan da aiki ya kaimu na je fadar shugabannin ƙasashensu, kuma mun gana da shugabannin ƙasashen da manyan ‘yan kasuwar ƙasashen, na yi tafiya a cikin jirgin shugaban ƙasa a lokacin Obasanjo na shugaban ƙasa, na yi tafiya tare da shi a cikin jirgi ɗaya inda muka ziyarci wasu ƙasashe na duniya don neman a yafe wa Nijeriya bashin da ake binta. Don haka ko na tsaya takara ko ban tsaya ba ina tare da shugabannin siyasa kuma su kan nemi shawarata.

Kasancewar Nijeriya ta cika shekara 61 da samun ‘yancin kai, ko akwai wani cigaba da ki ke ganin ƙasar ta samu a cikin waɗannan shekaru?
Idan aka ce mutum ya cika shekara 61 za a iya cewa ya girma kuma ya mallaki hankalin kansa, a lokacin da nike yarinya ba bu ma’aikatu kamar haka, babu hanyoyi kamar haka, babu fasahar zamani kamar yanzu, babu motoci ko tituna kamar haka, babu ilimi da cigaba kamar yanzu, saboda haka an samu cigaba sai dai ci gaban bai kai yadda ake zato ba a wannan shekaru da Nijeriya ta samu ‘yancin kai. Rashin isasshen ci gaba yasa ake ma Nijeriya kallon tana gaba ta na baya.

Ya ki ke kallon aikin gwamnati a shekarun baya idan aka kwatanta da wannan lokacin?
Kasancewar na yi aikace-aikace a baya kuma har yanzu ina cikin yin wa su ayyukan zan iya cewa a ‘yan shekarun baya an fi yin aiki tuƙuru, kuma an fi yin aiki da gaske da mai da hankali, amma yanzu kasancewar akwai ci gaban zamani kusan komai ya koma a kan kwamfuta, shiyasa ma’aikata ba su fiye dagewa ba su yi aiki kamar yadda ake yi a shekarun da ba bu fasahar zamani saboda yanzu aiki ya fi sauƙi ga sauri idan aka kwatanta da can baya.

Hajiya Mariya

Wacce shawara za ki ba wa ‘yan uwanki mata?
Duk macen da ta san bata da ilimin da za ya taimaka mata don ta cimma burinta na rayuwa ya kamata ta dage ta nemi ilimin, ba a girma da neman ilimi saboda sai da ilimi ake gudanar da rayuwa. Ya kamata mata su dinga sauraren radiyo da talabijin ko kuma su dinga karanta jaridu don sanin abinda duniya take ciki, ba a son mace ta zauna da duhun kai, bayan nan mace ta sa ido akan ‘ya’yanta, ta dage da ba su tarbiyya don su zama masu taimakon al’umma. Ina kuma ba mata shawara da su dage su nemi sana’a koda mace ta yi karatun boko ba lallai ba ne ta samu aikin gwamnati ba a yanzu, saboda abin ya yi yawa, don haka ya kamata ta tashi ta nemi sana’a don taimakawa kanta ko ‘ya’yan ta da ma mai gidanta.

Batun iyali fa?
Na yi aure tun Ina makarantar sakandare. Yanzu ina da ’ya’ya guda biyar da jikoki.

Waɗanne ƙalubale ki ka fuskanta a rayuwarki?
Ƙalubalen da na fuskanta a rayuwa ko a aikace-aikacen da na yi bai wuce na ce aikin jarida ya na ɗaukar lokaci saboda wani lokacin sai ka kusa kwana a ɗakin shirya shirye gashi ina da aure da yara ga kuma kula da gida, ƙalubale ta fannin siyasa kuma shine za ka ga maza ne su ka mamaye harkar siyasa wanda ba ƙaramin ƙalubale bane ga mace ta kasance a wajen da aka ce maza ne suka fi yawa, sai dai na yi sa’a kasancewar ni da maigidana aiki iri ɗaya muke yi to ƙalubalen ya zo da sauƙi. A kowane irin ƙalubalen rayuwa idan ka fahimci ƙalubalen za ka fi sanin hanyar magance shi cikin sauƙi.

Waɗanne nasarori ki ka fuskanta ta fannin rayuwa ko kuma aikace aikacen da ki ka aiwatar?
Alhamdu lillah na sami nasarori da yawa, kamar yadda na gaya maka a baya duk wanda ya ji an ambaci sunana sai ya yi tunanin na tara miliyoyin kuɗi amma sunan ne kawai wanda a wurina babbar nasara ce, damar da na samu na haɗuwa da shugabannin ƙasashen duniya shima nasara ce, hakan nan ma muƙaman da na riƙe shima nasara ce a gare ni, bayan haka ziyartar gidajen shugabannin ƙasashe kamar ‘White House’ da sauran su duk nasara ce a gare ni, bayan nan ko bani da rai za a dinga tunawa da ni a matsayin mace wacce ta ke son cigaban mata da matasa shima ina kallonsa a matsayin nasarar da na samu a rayuwa.

Hajiya, mun gode sosai.
Ni ma na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *