Ruftawar bene: Mutane 10 sun rasa rayukansu a Legas

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Aƙalla mutane 10 ne aka ruwaito sun mutu a ranar Litinin bayan da wani gini mai hawa 21 ya ruguje a hanyar Gerard a unguwar Ikoyi da ke Jihar Legas.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, mutane da dama sun maƙale a cikin baraguzan ginin, ciki har da Manajan Darakta na Fourscore Heights Limited, Femi Osibona, wanda shi ne mai maginin, da wasu abokan aikinsa da injiniyoyi.

Ɗaya daga cikin ma’aikatan da suka tsallake rijiya da baya, Gabriel Bassey, ya shaida wa manema labarai cewa, har yanzu kimanin mutane 50 ne ke maƙale a cikin ɓaraguzan ginin.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Legas, Hakeem Odumosu, ya tabbatar da mutuwar mutane biyar, inda ya ƙara da cewa an ceto wasu uku.

Sai dai kodinetan hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa reshen kudu maso yamma, Ibrahim Farinloye ya ce, an gano gawarwaki huɗu a ginin, inda ya ce, an ceto wasu huɗu.

Kwamishinan yaɗa labarai da dabarun Jihar, Gbenga Omotosho, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce, jami’an ceto na nan a ƙasa domin ceto waɗanda ke ƙarƙashin ɓaraguzan ginin.

Ya ƙara da cewa, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin, inda ya ce za a bayyana rahoton binciken.

Ma’aikatar tsare-tsare da raya birane ta Jihar a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ta ce, an fara bincike don gano musabbabin rugujewar ginin.

Sanarwar ta ƙara da cewa, manyan manajojin hukumar kula da gine-gine ta Jihar Legas da hukumar ba da izinin tsara gini ta Jihar Legas suna nan a ƙasa domin tantance irin ɓarnar da aka yi wa gine-ginen, idan akwai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *