Kotun Ƙoli ta yi magana kan mamaye gidan Mai Shari’a Odili

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

A ranar Talata ne kotun ƙolin ƙasar nan ta bayyana mamaye gidan mai shari’a Mary Odili da cewa ba a hukunta shi ba.

A martaninta na farko kan wannan mummunar lamarin, kotun ƙolin, a wata sanarwa da kakakinta, Akande Festus, ya fitar, ta ce harin rashin wayewa ne, kuma abin kunya ne na farautar wani jami’in shari’a da ba shi da laifi.

Kotun ta yi gargaɗin cewa bai kamata wani mutum ko ma’aikatun gwamnati su yi wa ɓangaren shari’a mummunar fahimta a matsayin yaron da ake yi wa bulala a cikin hannun gwamnati uku ba.

Sanarwar wadda aka karanta a wani ɓangare ta ce, “mun firgita da labarin yadda aka kai wani samame ba bisa ƙa’ida ba da kuma wulaƙanci da aka kai gidan wani babban alƙalan mu a kotun ƙoli, Hon. Mai shari’a Mary Peter Odili, a ranar Juma’a 29 ga Oktoba, 2021, ta hanyar Gestapo.

“Harin abin baqin ciki ya nuna wani mummunan hoton yaƙi da wasu mutane ɗauke da makamai da ake zargin jami’an tsaro ne da ke wakiltar hukumomin gwamnati daban-daban waɗanda da alama sun zo ne domin kashe su da kuma lalata musu abin da suke nufi da fakewa da gudanar da bincike wanda sammacinsa abin tambaya ne kuma marar tushe,” inji sanarwar.

Sanarwar ta qara da cewa, “muna matuƙar baƙin ciki da mamakin wannan rashin wayewa da abin kunya da aka nuna wa jami’in shari’a da ba ta da wani laifi da ta kwashe shekaru da dama a rayuwarta mai albarka tana yi wa ƙasarta hidima.”