An cafke mamallakin benen da ya ruguje a Legas saboda saɓa ƙa’ida

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babban Manajan Hukumar Kula da Tsarin Gine-gine a Jihar Legas (LASBCA), Gbolahan Oki ya ce mamallakin benen nan wanda ya ruguje mai hawa 21 da ake ginawa a Ikoyi, an ba shi izinin gina hawa 15 ne kawai.

Oki ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ta wayar salula cewa hukuma ta cafke mai gidan, kuma zai fuskanci shari’a saboda rayukan mutane da suka salwanta a dalilin iftila’in.

“Ya samu izinin gina bene mai hawa 15, amma sai ya ƙara yadda yake so. Yanzu haka ina a wajen, hatta kayan aikin da aka yi ginin ba masu nagarta ba ne.

“Kayan gini sam ba su ƙwari aka yi amfani da su ba, akwai haɗari sosai. Asali kuma ya samu izinin gina bene ne mai hawa 15, amma sai ya yi gaban kansa ya ɗora hawa 21. “Yanzu haka ma an kama shi, an rufe,” ya ce.

Manajan hukumar gine-gine ta Jihar Legas ya ce mutane huɗu ne ake ceto rayuwarsu, yayin da uku suka mutu, ya ce kuma ana ci gaba da ceto rayukan su.

Aƙalla dai mutane 50 ne aka bayyana cewa sun maƙale a bene mai hawa 21 da ya ruguje a Ikoyin Jihar Legas. Ginin mai lamba 20 kan titin Gerrard ya ruguje ne ranar Litinin da misalin ƙarfe uku na rana.