Mun kama waɗanda suka kai samame gidan Mai Shari’a Mary Odili – Sufeto Janar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An kama mutanen da suka kai samame gidan Mai Shari’a Mary Odili ta Kotun Ƙoli da ke Abuja, kamar yadda Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Usman Alkali Baba ya bayyana.

Alkali ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da Mataimakin Sufeton ‘Yan Sandan shiyya ta biyu a wajen taron sanin makamar aiki da aka shirya wa jami’an tsaro a Legas da kuma Ogun, wanda ya gudana a Victoria Island cikin birnin Legas.

Bayan irin kiraye-kirayen da jama’a ke ta yi akan wannan badaqala, ranar Litinin Babban Sufeto Janar na ‘Yan sandan Nijeriya ya an kama jami’an tsaron da suka kai farmaki gidan mai shari’ar.

“Na ɗauki lokaci ina magana akan wannan al’amari domin ganin an samar wa ‘yan Nijeriya da cikakkun bayanan da muka samu,” cewar Usman Baba da yake bayyana ci gaban da suka samu.

“Zan yi bakin ƙoƙarina wajen ganin an hukunta masu laifin da kuma gano dalilin da ya sa suka kewaye wa mai shari’ar gida da sunan ƙwacewa.”

Ranar Juma’a da dare ne dai jami’an tsaro su ka kewaye gidan Mary Odili, amma jami’an tsaron gidan ta su ka ce ba za su shiga ba, sai da sammacin kotu.

Mary Odili dai ita ce matar tsohon gwamnan jihar Delta Peter Odili, wanda ya shafe shekaru da dama yana kulle-kurciya da EFCC. Tun bayan saukar da gwamna cikin 2007 ya ke garzayawa kotu ana ba shi kariyar hana EFCC su bincike shi ballantana a gurfanar da shi.

Wasu rahotanni sun nuna cewa Mary Odili ta shaida wa jami’an tsaron cewa ba za ta bari su shiga gidan ta ba, saboda ba gidan mijin ta Peter Odili ba ne, gidan ta ne.

A hannu guda kuma dama Kwamitin Majalisa mai lura da vangaren shari’a ya nemi gwamnati ta yi ƙwaƙƙwaran bincike domin gano duk masu hannu wajen shirya makircin da jami’an tsaro suka kai gidan Mai Shari’a Mary Odili ta Kotun Ƙolin Nijeriya.

Shugaban Kwamitin Shari’a na Majalisar Tarayya, Luke Onofiok dama ya ce ya zama tilas a gano dukkan masu hannu domin a hukunta su.

Ya ce irin wannan abin takaici da abin kunya da ya faru, ya na rage wa sashen shari’a kima, martaba da daraja ne a idon ‘yan Nijeriya da idon duniya baki ɗaya.

Duk da cewa mijin ta Peter Odili ya na da matsala da EFCC, har ita EFCC ɗin ta sa Hukumar Shige da fice ta riqe masa fasfo ɗin sa, amma EFCC ɗin ta ce babu hannun ta a farmakin da jami’an tsaro su ka kai gidan matar sa.

Haka shi ma Ministan Harkokin Shari’a, Abubakar Malami ya nesanta kan sa ko hannun ma’aikatar sa daga farmakin da jami’an ‘yan sandan su ka kai gidan Mai shari’ar, a cikin wata sanarwa da Umar Gwandu wanda shi ne Kakakin Yaɗa Labarai na Minista Malami, ya bayyana cewa, “dirar mikiyar da jami’an tsaro su ka yi a gidan Mai Shari’a Mary Odili, akwai alamu na tantagaryar iskanci wajen ƙulla shirin.