Ruben Amorim ya yi amai ya lashe kan kalaman da ya yi cewar ƙungiyarsa ta Manchester United ta kakar nan ita ce mafi muni a tarihi.
Sai dai ya ce ba zai yi yaudara ba da cewar ba su da manyan matsaloli ba a kasa.
Amorim ya ce ya yi kuskure da ya samar da baraka lokacin da ya fuskanci ’yan wasa nan take, bayan tashi karawar da Brighton ta yi nasara 3-1 a Premier League.
Hakan ya sa ya gana da ’yan jarida cikin fushi da ta kai ya faɗi wasu kalaman.
An tambaye shi ko ya san cece-kucen da batunsa ya haifar kafin fuskantar Rangers a Europa League, Amorin sai ya ce yana magana da kansa ba da ’yan wasa ba.
Sai dai ya amince da dukkan sakamakon da ya faru a Man United tun bayan da ya kama aiki a cikin Nuwamba – Ya samu maki 11 da rashin nasara shida daga wasa 11 a Premier League – wannan ba abin a yaba bane.
”Ina magana da kaina fiye da ’yan wasa, kamar yadda Amorim ya ce ”Amma wasu lokutan yana da wuya na voye fushi na.”
United tana gurbin da za ta iya kai wa zagayen ’yan 16 a Europa League kai tsaye, an fitar da ita a League Cup, kuma tana ta 13 a teburin Premier League.
Har yanzu akwai batun da ake tambaya kan dakikin da United ba ta ƙoƙari a gida, wadda aka doke wasa huɗu daga biyar da ta yi baya.
An doke United wasa shida daga 12 da ta yi a Old Trafford a Premier League – ƙwazo mafi muni tun bayan 1893-94.
Watakila United ta fuskanci wasannin gaba da kwarin gwiwa, saboda mai tsaron baya, Victor Lindelof ya koma atisaye bayan jinya, haka shima Marcus Rashford ya fara karvar horo, wanda ake alakanta shi da wasu ƙungiyoyin.
