Matsalolin Nijeriya na hana ni barci – Sarkin Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, ya bayyana cewar matsalolin da Nijeriya ke fuskanta na daga cikin abubuwan da ke hana shi bacci ido biyu rufe.

Ya bayyana haka ne a fadarsa da ke Birnin Katsina, lokacin da yake ƙaddamar da gidauniyarsa mai laƙabin ‘Gidauniyar Mai Martaba Sarkin Katsina’.

“Matsalolin Nijeriya na daga cikin abubuwan da suka dame ni, har ta kai ina rasa bacci, nakan yi kwana uku zuwa bakwai ba na bacci,” inji shi.

Basarken ya kuma ce matsaloli gami da ƙalubalen ƙasar nan, su ne suka haddasa masa larura ta rashin lafiya.

“Waɗannan abubuwan su ne suka haddasa mani iftila’in da na shiga na yanayin lafiyata.”

A cewarsa, ya yi tunanin kafa wannan gidauniya ne cikin mako ɗaya, don tallafa wa waɗanda iftila’in harin ‘yan ta’adda ya shafa a ƙananan hukumomin jihar.

Ya ƙara da cewa, yana shirye-shiryen ƙaddamar da gidauniyar sai ya gamu da wata larura, lamarin da ya sa aka dakatar da ƙaddamarwar sai bayan da ya dawo daga Landan.

Yana mai cewa, ya zaɓi ƙaddamar da gidauniyar cikin watan Ramadan ne saboda shi ne fiyayyen wata a cikin watanni.

Daga nan ya buƙaci masu hannu da shuni a kan su shigo don bada tallafinsu ga gidauniyar.

A ƙarshe, ya yi addu’ar samun zaman lafiya a Jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya.

Aƙalla mutane 17,000 ne suka amfana da tallafin wanda ya ƙunshi buhunan shinkafa, masara, gero, sukari da kuma tufafi.

Shugaban amintattu na ƙungiyar kuma Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Ida, ya ce sarkin Katsina Alhaji Abdulmumin Kabir Usman ne ya kafa gidauniyar, yake kuma bada tallafi a ɓoye sai dai bayan wani zama da Sarkin ya yi da ‘yan majalisarsa a Kaduna sun yanke shawarar faɗaɗa ta.

Ya kuma ce maƙasudin kafa gidauniyar shi ne don tallafa wa ƙoƙarin gwamnati wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Da yake jawabi a madadin ƙananan hukumomin jihar da suka amfana da tallafin gidauniyar, Yariman Katsina kuma Hakimin Safana, Alhaji Sada Rufa’i, ya gode wa Sarkin dangane da kafa gidauniyar don taimaka wa al’umar jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *