Gwamnatinmu na da sauran lokaci a Kano, Ganduje ga Abba

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Gwamnat Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Uamar Abdullahi Ganduje, ta yi kira ga Gwamnan jihar mai jiran gado, Engr. Abba Kabir Yusuf, da ya yi haƙuri tare da daina fitar da sanarwa a hukumance ta hanyar ba da shawara ga jama’a domin kada a haifar da ruɗani da bai kamata ba a jihar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Malam Muhammad Garba, ya fitar a ranar Juma’a a matsayin martani ga umurnin da ofishin zababben gwamnan ya fitar, inda ya gargaɗi mutane, ƙungiyoyi da ƙungiyoyin da suke gudanar da gine-gine a wuraren taruwar jama’a da su kiyaye.

Sanarwar ta ce matakin da zaɓaɓɓen gwamnan ya ɗauka ya kai ga yin tsalle-tsalle ta hanyar bayar da umarni kan lamarin da ya shafi manufofin gwamnati alhali Gwamna mai ci bai cika wa’adin mulkinsa ba.

Muhammad Garba ya bayyana cewa, dangane da batun rabon muƙamai kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya ya tanada, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ci gaba da zama gwamna mai ikon zartarwa har zuwa ranar 29 ga watan Mayu kuma yana da haƙƙin gudanar da ayyukansa a maslahar jama’a ko wani abu mai kama da hakan.

“Har sai ya zama gwamna a ranar 29 ga Mayu, ya ci gaba da zama zaɓaɓɓen gwamna kuma ba shi da ikon gwamna, abin da kawai zai iya yi shi ne ya mayar da wasu ayyukan da magabatansa ya yi a lokacin da ya hau kan karagar mulki idan har akwai ƙwararan dalilai na yin hakan.

“Babu wani zaɓaɓɓen gwamnan da yake da ikon tsarin mulki ko doka na tantance alƙiblar jihar har sai an rantsar da shi.”

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnonin jihohi suna da iko da yawa wajen rabon filayen, don haka kowace gwamnati ta yi irin wannan aiki ciki har da gwamnatin da ta shuɗe wacce zaɓaɓɓen gwamnan ya yi aiki.

A cikin sanarwar ya ce bisa ga bayanan da ake da su, gwamnatin da ta shuɗe ta yi rabon filayen a wasu wuraren taruwar jama’a da zaɓaɓɓen gwamnan ya ambata da suka haɗa da katangar birnin, tare da raba fili daga Ƙofar Nassarawa zuwa Ƙofar Mata, shaguna a filin Sallar Idi na Ƙofar Mata da ke fuskantar gidan sinimar Orion da kuma daga Ƙofar Mata zuwa ‘Yan Yashi daura da filin Idi, sai kuma daga Ƙofar Kabuga zuwa Ƙofar Famfo da ke fuskantar tsohon Campus na Jami’ar Bayero.

Muhammad Garba ya bayyana cewa shawarwarin da zaɓaɓɓen gwamnan ya bayar ya haifar da tashin hankali a jihar inda ya shawarce shi da ya haƙura da hakan domin gudun kawo ruɗani.

Daga ƙarshe, ya yi kira ga mutane da ƙungiyoyi da suka mallaki fili bayan bin ƙa’idoji da tsare-tsare da kada a yi barazana da umarnin.