Daga AISHA ASAS
Fitaccen mawaƙin Hausa, Ali Jita kuma ɗaya daga cikin jiga-jigan magoya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fice daga Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) inda ya yi sabon masauki a jam’iyyar adawa ta APC.
Kamar yadda rahotanni da dama suka ruwaito, Jita ya fice daga jam’iyyar Gwamna Yusuf, NNPP a ranar Alhamis, matakin da ke nuni da janye goyon bayansa ga gwamnan Jihar Kano.
Mawaƙin ya samu tarba ne a Jam’iyyar APC ta hannun mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ɗan majalisa mai waƙiltar Kano ta Arewa.
Da yake karɓar mawaƙin, mataimakin shugaban majalisar dattawan, ya bayyana zuwansa jam’iyyar APC a matsayin abin farin ciki.
“A matsayinsa na matashi kuma haziƙin mawaƙi, Ali Jita zai kawo ƙwarewarsa da gogewarsa a jam’iyyar, wanda zai share fagen bunƙasa harkar waƙa da masana’antar Kennywood bakiɗaya. ina yi maka maraba da zuwa babbar jam’iyya, ” inji shi.
Da yake nasa jawabin, Ali Jita, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar mawaƙan Kano da aka fi sani da Murya ɗaya, ya bayyana Sanata Barau a matsayin uba.
“Ta sanadiyar jagoran tafiyar ta jam’iyyar Kwankwasiyya na shiga jam’iyyar, wato Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
“Amma a yau na sauke jar hula, yanzu ba na cikin harkar jajayen huluna, yanzu ni cikakken ɗan Jam’iyyar APC ne,” a cewar sanarwar da Ismail Mudashir, kakakin Sanata Barau ya fitar.
“Ina so in tabbatar muku da cewa zan yi amfani da iyawa da basirata wajen bayar da gudunmawa a wannan tafiya, yanzu gidana ne APC, kuma jam’iyyata ce, za mu yi ƙoƙarin ganin ta samu nasara a gaba,” inji shi.
A ‘yan kwanakin nan ‘ya’yan jam’iyyar NNPP, waɗanda su ma magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya ne ke ta tururuwa zuwa ga ɓangaren Sanata Barau, inda suke tuhumar tsohuwar jam’iyyar tasu da ƙin ba su ladan goyon bayan da suka bayar.
A kwanakin baya dai wasu fitattun ‘yan Jam’iyyar NNPP ‘yan Kwankwasiyya irin su Sharu Habu Tabule da Rabiu Daushe suka fice daga jam’iyyar da kuma shigewa Jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin Sanata Barau.
Rahotanni da dama sun bayyana yadda wasu jiga-jigan Kannywood da suma suka fito fili suka nuna rashin jin daɗinsu ga tafiyar ta Kwankwasiyya, kamar jarumi Garzali Miko da Hafsat Muhammad da furodusoshi Salisu Officer, da sauransu.
