Mayaƙan ISWAP biyar ciki har da Larabawa sun rasu yayin ƙera boma-bomai a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mayaƙan ƙungiyar ISWAP guda biyar ciki har da wani da ake zargin jami’in lafiya ne da wasu huɗu waɗanda ƙwararru ne wajen ƙera ababen fashewa (IEDs), sun rasu a lokacin da suke ƙoƙarin haɗa boma-bomai a Ƙaramar Hukumar Marte ta Jihar Borno.

A ranar Talata masanin harkar tsaro, Zagazola Makama ya sanar da faruwar al’amarin, wanda ya auku a ƙauyen Maina Daya da ke tsakanin Sabon Tumbu da Jubilaram, kusan kilomita 29 daga gabashin Ƙaramar Hukumar Monguno da ke Borno.

A cewar majiyoyi, al’amarin ya yi ajalin Usman Ɗan Fulani da aka bayyana a matsayin jami’in lafiya na ISWAP tare da wasu Larabawa biyu masana harkar haɗa boma-bomai da wasu mayaƙa biyu waɗanda su ma ƙwararru ne wajen haɗa bom.

Majiyoyin sun bayyana cewa, iftila’in ya auku ne a lokacin da mayaƙan suke ƙoƙarin haɗa boma-bomai domin rabawa a hanyoyin da sojojin Atisayen Haɗin kai ‘yan Sashe na 1 suke safarar kayayyakinsu.

Masanin ya kuma ce hakan wani babban koma-baya ne ga fannin ƙera boma-boman ƙungiyar wanda kuma ka iya kassara ayyukansu na tayar da boma-bomai a yankin Marte da Monguno.

Majiyoyin sojoji sun ce an umarci dakarun Haɗin Kai da su yi amfani da damar ci-gaban wajen ƙaddamar da atisayen ‘cordon-and-search’ da hare-hare a yankin Monguno, Marte da Gamboru Ngala domin hana ‘yan ta’addar sake gina ƙarfinta na ƙera ababen fashewar.

By Babaji

Leave a Reply