Rayuwa bayan ritaya: Tsari a ilimance don samun ingantacciyar rayuwa na biyu

Spread the love

Tare da BILKISU YUSUF ALI P’hD

Cigaba daga makon da ya gabata

Gabatarwa

Kamar yadda muka faɗa a baya cewa “ritaya wani mataki ne na rayuwa da kowane ma’aikaci zai iya fuskanta idan Allah Ya ba shi tsawon rai. A mafi yawan lokuta, mutane suna shiryawa ne domin samun aiki, samun albashi da gina iyali, amma ba sa bai wa rayuwa bayan ritaya muhimmancin da ta dace. Wannan rashin shiri kan haifar da matsalolin tattalin arziki, damuwa ta tunani, matsalolin lafiya da kuma rashin walwala”. Masana ilimin zamantakewa da tattalin arziki sun nuna cewa shiryawa tun kafin ritaya yana taimakawa mutum ya ci gaba da rayuwa cikin mutunci, kwanciyar hankali da walwala.

Matsalolin da masu ritaya ke fuskanta

Akwai matsaloli da sukan zama ruwan dare ga waɗanda suka yi rirata wanda wannan ne ma yake janyowa a ji tsoron juyin rayuwa bayan gama aiki ko yin ritaya. Wasu matsalolin na ɗabi’a ne wasu kuma matsalolin mutane ne suke ƙirƙira ko don rashin sani ko don ganganci.  Daga cikin waɗannan matsaloli da suka zama gama-gari akwai:-

Rashin isasshen kuɗi

Kasancewar lokacin da mutum yake aiki yana samun albashi yana iya samun wasu damarmaki a wurin aiki wannan ya sa lokacin da aka bar aikin wannan albashin ya tsaya haka damar ta tsaya dole yadda ake mu’amala da kuɗi ta baya. 

Jinkirin biyan fansho.

Shi ma jinkirin biyan kuɗin fansho ga ma’aikacin da ya bar aiki babbar matsala ce don shi ne yake maye gurbin albashi kuma bai kai albashin ba kuma ba ma a samunsa akan lokaci saboda sakacin hukumomi da kuma tsare-tsare na hukumar fanshon.   

Rashin lafiya.

Yau da gobe sai Allah, haka kuma jiki da jini musamman ma lokacin da aka yi ritaya shekaru sun ja. Akwai dalilai da dama da suke janyo larura ta rashin lafiya akwai na damuwa da na shekaru wanda kowanne matsala ce mai zaman kanta kuma barazana ne ga lafiyar mai ritaya. 

Kaɗaici

Sau tari lokacin da shekarun ritaya suka riski mutum a daidai wannan lokacin iyali wasu sun yi aure ɗawainiya ta kuma riɓanya ta gwagwarmayar iyalin sannan wasu sun bar gida sun kama gabansu, ita kuma mace a wannan lokacin hankalinta ba yana kan mijin ba ne ita ma yana kan ganin ginuwar iyalinta da tare matsalolinsu sai ya zamana an bar mijin da kaɗaici da rashin abokanan hira a gida da na mu’amala. Wannan kaɗaicin yana damun mai ritaya kwarai da gaske wataƙila ma gidan fashewa ake yi a bar maigidan shi kaɗai. 

Damuwa

Akwai damuwa musamman ga wanda ya saba fita kullum ya je ya dawo ya yi mu’amala da mutane amma lokaci guda a ce wannan zirga-zirgan an daina sai dai a dawo a zauna. Wataƙila ma akwai abubuwan da aka faro ba a ƙarasa ba kuma ake da buri, rashin ƙarasawar yana iya kawo damuwa. Haka rashin zuwa aiki da zaman gida musamman in ba a samu wata sana’a ba duka suna iya haddasa damuwa.  

Dogaro da yara

Duk lokacin da za ka dogara da wani dole akwai ɓacin rai. Iyaye lokacin da ƙarfinsu ya ɗauko ƙarewa suna ɗora wasu nauye-nauye akan yaransu. Saɓani kan shiga kuma sau da yawa na rashin fahimta ne sai iyaye su ke kallon yaransu ba sa yi musu hidima ko wadda suke yi ta yi kaɗan. Haka wasu yaran suma suna kasa jure ɗawainiyar iyayen. 

Hanyoyin magance matsaloli

Babu wata matsala da za a ce ta zo dindindin saboda akwai maganinta sai dai in har ba a tare ta akan lokaci ba. Manyan hanyoyin kawo ƙarshen matsalar ritaya da wasu suke samun kansu a ciki akwai: 

Gwamnati

Gwamnati tana da rawar da za ta taka kwarai da gaske wajen ta ragewa mai yin ritaya nauyi da damuwa ta yadda ba zai shiga wani mayuwacin hali ba bayan ya yi ritaya ba. Daga cikin abin da zai rage raɗaɗi akwai biyan fansho a kan lokaci da inganta tsarin inshorar lafiya.da horas da ma’aikata kafin ritaya. Sannan a yi tsari na samar da rancen kasuwanci ga masu ritaya.

Ma’aikata

A ɓangaren ma’aikata suma suna da rawar takawa da kuma yadda ya kamata su shirya tun daga ranar da suka fara aikin har zuwa ranar ritaya. Wajibi ne su fara tanadi tun suna aiki, su guji almubazzaranci, su nemi ilimin juya kuɗi. Su mallaki kadarori masu amfani.

Iyali

Suma iyali suna da rawar takawa lokacin da maigida ya yi ritaya. Ya kamata su mutunta masu ritaya su ja su a jiki su mutunta su, suke ɗebe musu kewa ta damuwa da kaɗaici. Haka suke tallafa musu da abin da ya samu daidai gwargwado. Mata su sani lafiya da kwanciyar hankalin iyalinsu yana tattare da mazajensu don haka lokacin ritayar maigida lokacin kula da shi ne da ba shi kariya sannan su saurare su. Sannan s u yi amfani da gogewarsu wajen tarbiyya.

Rayuwa Bayan Ritaya a Mahangar Ilimin Zamantakewa

Masana ilimin zamantakewa sun bayyana cewa ritaya tana da matakai:

Farin cikin samun hutu.

Jin rashin aikin da aka saba.

Daidaitawa da sabon yanayi.

Gina sabuwar rayuwa.

Mutanen da suka shirya tun kafin ritaya sukan fi samun walwala da kwanciyar hankali.

Kammalawa

Rayuwa bayan ritaya ba ƙarshen rayuwa ba ce, sabon mataki ne da ke buƙatar shiri mai kyau. Duk wanda ya fara tanadin kuɗi da kula da lafiya da ilimi da neman sana’a da gina  iyali da riƙo da addini tun kafin ya yi ritaya, zai samu damar rayuwa cikin mutunci da farin ciki. Don haka, ya zama wajibi gwamnati da cibiyoyin ilimi da  ma’aikatu da iyalai su haɗa kai wajen wayar da kan ma’aikata kan muhimmancin shiryawa tun kafin ritaya domin gina al’umma mai ɗorewa.

Manazarta (References):

Atchley, R. C. (1989). Retirement: Leaving the World of Work.

World Health Organization (WHO). Healthy Ageing Framework.

United Nations. World Population Ageing Reports.

International Labour Organization (ILO). Social Protection and Pensions.

Federal Republic of Nigeria. Pension Reform Act (2014).

By ukarofi

Leave a Reply