Mazauna Abuja na fuskantar matsanancin matsalar fetur

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Yawancin masu ababen hawa a Babban Birnin Tarayya Abuja, na fuskantar matsalar man fetur da dogayen layuka ake cigaba da yi a gidajen man.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya da ya sa ido a gidajen mai a Abuja a ranar Talata, ya ba da rahoton cewa, yawancin gidajen fetur ɗin a rufe suke, yayin da kaɗan ne kawai ke badawa, wanda ya haifar da mummunar cunkoson ababen hawa saboda dogayen layukan da ake yi.

Masu motocin sun kuma nuna rashin jin daɗinsu kan ƙarancin tsabar kuɗaɗen da ake samu a ƙasar nan, wanda suka ce yana ƙara ta’azzara lamarin, inda suka yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sa baki.

Kamfanin Mai na Nijeriya (NPL) ya danganta layukan man fetur a Abuja da wasu sassan ƙasar da taƙaita harkokin kasuwanci da zirga-zirga a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar dokoki ta ƙasa.

Hukumar ta NNPC ta ce, an koma aiki a gidajen man kuma ana jigilar manyan motocin mai zuwa sassa daban-daban na ƙasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *