Dillalan hatsi sun ƙi amincewa da tiransfa a Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Dillalan hatsi a kasuwannin bayan gari a Babban Birnin Tarayya, Abuja, na ƙin amincewa da hada-hadar kuɗi na tiranfa daga kwastomomi, duk da ƙarancin tsabar kuɗi na babban bankin Nijeriya, CBN.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya da ya sa ido a kasuwannin Nyanya, Karu, Mararaba da Masaka a ranar Talata a Abuja, ya lura ’yan kasuwar ba sa karɓan tiranfa sai tsabar kuɗi.

A cewar ’yan kasuwar, suna sayen kayayyakin ne kai tsaye daga hannun manoman karkara waɗanda ba su yarda da wani nau’i na hada-hadar banki na lantarki ba.

Kadijat Ibrahim, ’yar kasuwa a kasuwar Nyanya, ta ce duk da cewa yawan kwastomominta na raguwa, amma za ta ci gaba da neman tsabar kuɗi akan kayanta.

Ismaila Abu, wani ɗan kasuwan hatsi a Kasuwar Mararaba, ya ce ba ya karɓar duk wani nau’i na tiransifa na kayansa.

“Ina amfani da ɗan jari kaɗan don kasuwanci na kuma ba zan so na gudanar da shi a kowane banki ba.