Me ya sa mahalarta CAEXPO a bana ke sha’awar sake halartar bikin a shekara mai zuwa?

Daga CMG HAUSA

Kwanan nan wani jami’in ofishin kamfanin samar da kofi na ƙasar Vietnam dake birnin Shanghai na ƙasar Sin, ya ce yanzu suna da dillalai sama da 300 a ƙasar waɗanda ke taimakawa sayar da kofi.

An kawo ƙarshen bikin baje-kolin Sin da ƙungiyar ASEAN ko kuma CAEXPO, kana taron kolin Sin da ASEAN a fannin kasuwanci da zuba jari karo na 19, a jihar Guangxi ta ƙasar Sin a jiya Litinin.

A cikin kwanaki huɗu, kamfanoni 1653 na ƙasashe 40 sun halarci taron, har ma akwai kamfanoni sama da dubu 2 da suka hallara ta kafar intanet, inda aka ƙulla ayyukan haɗin-gwiwa 267, kana, jimillar kuɗin da aka zuba a waɗannan ayyukan ta kai kudin Sin Yuan biliyan 413, wanda ya kai matsayin koli a tarihi.

Ke nan an cimma nasarori masu tarin yawa a wajen bikin CAEXPO a bana.

A halin yanzu, tattalin arzikin duniya na fama da koma-baya, har ma asusun bada lamuni na duniya IMF, da sauran wasu cibiyoyin duniya, duk sun rage hasashen da suka yi, kan ƙaruwar tattalin arzikin duniya a bana da shekarar badi.

A irin wannan yanayin da ake ciki, shirya bikin CAEXPO na da ma’ana ta musamman.

A yayin da wasu ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki ke ƙoƙarin rufe kofarsu, ƙasar Sin ta gudanar da bikin CAEXPO, al’amarin da ya samar da sabbin damammaki ga farfaɗowar tattalin arziki, bayan da aka kawo ƙarshen annobar COVID-19.

Murtala Zhang