Fannin jigilar kaya na samun ƙaruwa a Ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA

Alƙaluman da aka samu sun nuna cewa, aikin jigilar kayayyaki a nan ƙasar Sin na samun karuwa, inda a jiya Litinin, yawan motocin dakon kaya da suka bi tagwayen hanyoyin ƙasar ya kai fiye da miliyan 7 da dubu 689, jimillar da ta ƙaru da kaso 11.43 bisa ta watan da ya gabata.

Ofishin kula da aikin jigilar kayayyaki dake ƙarƙashin majalisar gudanarwar ƙasar Sin ne ya gabatar da alƙaluman, wadanda suka nuna cewa, a jiya 19 ga wata, jiragen ƙasa sun kwashe kayayyakin da nauyinsu ya kai ton miliyan 11 da dubu 125 a ƙasar, kana yawan kayayyakin da suka bi ta tashohin jiragen ruwa daban daban da aka gudanar da bincike a kansu ya kai ton miliyan 33 da dubu 213.

A fannin jiragen sama masu dakon kaya kuma, an samu zirga-zirgar jiragen sama guda 501 a ƙasar a jiya Litinin, inda daga cikinsu akwai jiragen sama 362 da suka yi jigilar kayayyaki zuwa ƙasashen ƙetare.

Ban da wannan kuma, kamfanoni masu jigilar kayayyaki cikin sauri na ƙasar Sin baki ɗaya sun karɓi ƙunshi kimanin miliyan 337 a jiya Litinin, yayin da yawan kayayyakin da suka kai wajen da ake neman tura su ya kai kimanin miliyan 312.

Mai fassara: Bello Wang