Wakilin Sin ya yi kira ga ɓangarori daban-daban da su aiwatar da shawarar tsaron ƙasa da ƙasa a majalisar kare haƙƙin bil’adam

Daga CMG HAUSA

Wakilin Sin ya yi jawabi a taron majalisar kare haƙƙin bil’adam karo na 51 da kuma taron tattaunawar masana masu zaman kansu a kan tsarin mulkin duniya bisa dimokuraɗiyya da adalci da aka gudanar a zauren majalisar kare haƙƙin bil’adam a jiya Litinin.

Yayin taron, ya yi kira ga ɓangarori daban-daban da su aiwatar da shawarar tsaron ƙasa da ƙasa, da aiwatar da ra’ayin ɓangarori daban daban.

Wakilin Sin ya bayyana cewa, ra’ayin ɓangarori daban daban, babban ra’ayi ne a tsarin duniya da kuma tsarin mulkin duniya.

Kuma ita ce hanyar kare zaman lafiya da kuma inganta ci gaba.

A cewarsa, kamata ya yi al’ummar duniya ta kare da kuma aiwatar da ra’ayin ɓangarori daban-daban bisa gaskiya, da adawa da ra’ayin danniya da kuma siyasar rukunoni tare kuma da adawa da takunkuman da wani ɓangare ɗaya ke ƙaƙabawa.

Har ila yau, ya bayyana cewa, ɓangaren Sin ya fitar da shawarar tsaron ƙasa da ƙasa, kuma ya gabatar da dabara don warware giɓin zaman lafiya da magance matsalar tsaro a duniya.

Yana mai cewa ita ce shawarar tsaron al’umma da Sin ta samar wa duniya.

Haka kuma, ya ce kamata ya yi ƙasa da ƙasa su tattaunawa da juna a maimakon nuna adawa, kuma su yi mu’ammala da juna a maimakon barazana, sannan su maye gurbin adawa da zumunci da maye gurbin nasarar gefe ɗaya da samun nasara tare.

Haka kuma, su aiwatar da ƙa’idar rashin rarrabuwar kawuna, da dora muhimmanci kan matsalolin tsaro na juna, da haɓaka gina tsarin gine-ginen tsaro masu inganci da ɗorewa.

Bugu da ƙari, ya ce ƙasar Sin tana son hada hannu da sauran ƙasashen duniya wajen kiyaye dabi’u guda na zaman lafiya, da samun ci gaba, da tabbatar da adalci, da dimokuraɗiyya, da ‘yanci ga dukkan bil’adam, da aiwatar da ra’ayin jama’a na haƙiƙa, da aiwatar da ayyukan tabbatar da tsaron duniya, da sa ƙaimi ga gina al’umma mai makoma ta bai daya ga bil’adam.

Mai fassara: Safiyah Ma