Me ya sa mazan suke gudun zaman gidajensu?

Daga AMINA YUSUF ALI

Assalamu alaikum. Sannunku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Manhaja. Sannunmu kuma da sake haɗuwa a wani makon mai albarka.

A wannan mako, muna tafe da bayani a kan rashin zama a gida da wasu maza suke yi. Sanan kuma da irin ƙorafe-ƙorafe da kuma matsalolin da matan waɗancan marasa zama a gidan suke fuskanta.

Kamar yadda mu ke iya gani a cikin zamantakewarmu, za mu ga akwai mazajen da ayyukansu da ma harkoki sukan ɗauke su daga gidajensu na yinin kowacce rana, wasu kuma ma aikin yakan ɗauke su daga garin kacokam ya kai su wani garin. Wasu kuma ba ayyukansu ba ne wasu dalilai ne daban suke ɗauke su daga gidajensu. Dalilan sun haɗa da:

Kamar yadda mu ka faɗa a gabatarwa, wasu mazan suna yin ayyuka ko sana’o’in da dole sai sun ɗauke su wuni suna yi. Walau aikin ofis ko kasuwanci. Wasu kuma sai sun bar garin suke aikin neman kuɗinsu. Wani ma sai ƙarshen mako zai dawo gidansa ko ƙarshen wata ko watanni.

Wani namijin kuma ba aiki ne ko sana’a ba. Yana da wuraren zuwa ne da ya saba da su. Kamar majalisa, ko masallaci ko gidan iyayensa ko tsohuwar unguwarsu da sauransu, idan ya dawo daga aiki. Wani kuma har wuraren neman mata ko wajen aikata alfasha kamar kulob ko wajen caca ko shaye-shaye da sauransu.

Amma akwai wasu da ba su da takamaimai wajen zuwa. Sun gwammace su yi ta gararambar gidajen abokai ko dangi a kan su je gidajensu. Saboda kawai gidan ne ba za su koma ba. Wasu ko dai ba su jin da]in gidan ko kuma kawai dai su a ganinsu zaman gida na mata ne da yara. Ko kuma suna ganin za a raina su idan matansu suka fiye ganinsu a gida. Shi ya sa sai su gwammace su yi ta zaga gari da su zauna a gidajensu.

Wannan halayya ta maza, mata sun kasa fuskantarta ko su amince da ita. Mata da yawa suna adawa da rashin zaman maza a gida. Masu magani da bokaye suna cin kuɗin mata a kan wannan matsalar. Mata da dama sun fi son ganin mazajensu a gida kamar yadda taurarin fina-finan da suke kalla, da na littattafan ƙagaggun labaran da suke karantawa suke yi. Kullum za a nuna namiji yana da kuɗi amma kullum yana gida yana maƙale da matarsa a kowanne hali. Shi ne taya ta girki da aikin gida da raino da sauransu.

Shin mata masu irin wannan tunani kun taɓa tunanin shi wannan tauraro fim ko littafi da yake zama a gida kullum yaushe yake fita neman da har ya tara waccan dukiyar da yake ta kashe wa matarsa da yi mata kyaututtuka na miliyoyi? Anya kuwa ba yaudarar kanku kuke yi ba? 

Wannan matsala ta rashin zaman magidanta a gida tana haifar da gingimemiyar matsala da zargi a tsakanin ma’aurata. Wata a shawo kanta, wata kuma sai dai a rabu idan an kasa fuskantar juna, ko an kasa yi wa juna uzuri. Dalilan da mata suka ce matsalar rashin zaman gidan maza tana kawo musu:

Na ɗaya, rashin samun isasshen lokacinsa yadda za su tattauna su yi hira. Ta nuna masa kwalliar da ta yi tun ba ta yi bacci ta tuje ta ba. Wani lokaci ma har a ɗan taɓa soyyayya irin wacce ake gani a fim ko littafi. Rashin hakan zai kawo rauni a soyayyarsu.

Na biyu, rashin zama a gidan yana sa ta zama aiki ya yi mata yawa. Ga aikin gida, ga tarbiyyar yara. Idan yana gida, zai kama mata wani abu. Ko yara yawanci sun fi jin tsoron uba a kan uwa. Wasu ma suna ganin galibi iyaye maza da ba sa zama a gida da masu tafiye-tafiye, yaransu sun fi lalacewa da rashin tarbiyya . Sai abin ya fi sauƙi idan suna ganin idon uban. Amma sai dai ba kowanne namiji ne zai yarda ya taya mace wani abu ba. Idan kin ci sa’a ma ya zauna a gida, sai dai ya je ɗakinsa ya yi ta bacci. Ba rini ba matsa, wai zaman kare a karofi.

Na uku kuma akwai matan da suke ƙorafin maza ba sa zama a gida kuma ba sa shaƙuwa da ‘ya’yansu. Wani uban sam bai saba da ubansa sosai ba. Saboda ƙarancin zamansa a gida. 
Sai na huɗu, wasu matan ma suna ganin rashin zaman maza a gida yana sa namiji ya koyi wasu salon ɗabi’u da zai wahalar rabuwa da su kamar neman mata, ko zuwa majalisa da sauransu. Musamman waɗanda an riga an san sana’arsu da ma ba ta kai wa daren ba ce. Irin waɗannan mata suna da matu}ar zargi da fargaba da binciken ƙwaƙƙwafi a kan ina mijinsu yake zuwa. Idan aka yi rashin dace garin tone-tone ta tono abin tashin hankali sai a samu matsala a aurensu.

Sai abu na gaba, mata suna ganin mazan da ba sa zaman aure suna ƙwararsu ta ɓangaren auratayya. Sai ya fice ya kai dare, ya dawo mata a gajiye ko iya ya same ta a gajiye. Yana dawowa sai bacci da munshari. Kuma washegari ya doka sammako. Ko kuma idan mai tafiya ne, sai dai ya zo ya kwana ɗaya, biyu ya wuce ba tare da ta amfanu yadda take so da zuwan nasa ba. Kuma wata ba ta iya faɗa masa ko iyayenta matsalar da take ciki. Saboda jin kunya irin ta mace.

Haka akwai matan da suke ganin rashin zaman gidan namiji yana sa ya ƙi cin abincinsu sai dai ya ci a titi. Wani ma ko rabin abinda yake ci a waje ba zai ajiye musu ba. Wani ma ba ya ba da komai sai dai ya yi sammako ya fice kuma ba zai dawo ba sai dare ya tsala.

Haka wasu mazan suna ficewa su bar mace da kewa. Musamman wasu amare ne da aka ɗauko daga wani gari ko ƙasa. Ba ta san kowa ba sai kai. Kai kuma ka fice tun safe. Wani kuma ya hana ta shiga maƙwabta. To ya za ta yi da ranta? Amma shawara irin waɗannan matan su nemi sana’a ko karatu, ko da islamiyya ce za ki ji kin rage kaɗaici.

Akwai irin dalilan nan suna nan, da mata suke ganin cutarwa ne a gare su. Har ma su dinga hange a maƙwabta da ƙawaye ko dangi yadda wasu mazan suke zaman gida abin har ya ba su sha’awa.

An san da gaske akwai maza masu ɗabi’ar son yawo. Su a ra’ayinsu kawai ba za su zauna a gida ba. Dole sai dai su fita. Akwai wani da na sani ko da ba shi da lafiya zai sa a ɗauke shi ranga-ranga a kai shagonsa na kasuwa. Kuma fa ba abinda zai amfana sai kwanciya. Amma shi bai saba da zaman gida ba ne a rayuwarsa.

Amma ‘yaruwa wacce mijinki ba ya zaman gida, kin ta~a zama kin yi tunanin meye ma dalilin da ya saba ya son zaman gidan? Ita fa kowacce matsala, in dai an gano mecece ita, to an samo maganinta. Ki daina ɓata lokaci bokaye da masu magani suna cinye kuɗinki. 

Sannan ki lura, su waɗancan mazajen da ba sa yawan fita kullum suna gida, wai sun fi mijinki nema da samu ne? Shi fa namijin nan da kike gani, shi ma yana son hutu. Ya fi ki buƙatar ma ya huta. Allah ya saka musu da alkhairi, duk yadda suke buƙatar hutu, idan suka tuno da buƙatar iyalansu, dole su fita su nema. Ba don kansu ba.

Ita rayuwar fim da littafin labaran hasashe ne kawai ake kamanta shi da gaskiya. Kuma ana masa ƙari don ku ji armashin kallo ko karatu. Wani namijin kuma halinki na ƙorafi ne ko ƙazanta da rashin gyara ke korar sa daga gidan. Ko kuma rashin jin maganarki yana magana sai fa]a. Hakan yana korar sa. Shi kuma ba zai zauna a gida ya gyara bai faɗa ba. Haka rashin kwalliya da kulawa yana hana namiji ya ji karsashin dawowa gidansa da wuri.

Wani kuma nutsuwa yake so, ya huta. Amma yara ba za su bar shi ba ya ko  runtsa ko kuma ya yi wani aikin.  Wani kuma aikinsa ne sai haƙuri. Ba ya ma zama a garin gabaɗaya. Zaman gida na mata ne. An riga an raba. Su su fita su nema, ke kuma ki tsare gida. Kuma ki kula masa da kanki da dukiyarsa. Kada ki ci amanarsa a bayan idonsa. Ke kuma mai zargi na yana neman mata, idan da rabon auren wata kin isa ki hana? Ki gama tashin hankalinki kuma ya auro. Ai ba haramun ba ne, ƙarin aure.

Ki sani haƙƙin kula da ku yana wuyansa. Idan ya zo ya zauna miki a gida soyayyyar za ku ci? Ko kuwa idan ya zauna a gidan ke za ki fita ki nemo? Don Allah mata a rage wannan yarintar haka.

Kai kuma mai zaman majalisa ka sani, ka kasance tare da matarka ku faranta ran juna ya fi alfanu da lada a kan wannan zaman kwasar zunubi da kuke yi a gefen hanya. Ku yi ta zancen mutane kuna kalle masu bin hanya, mata da maza. Can kuma ka bar matarka da ka ɗauko daga danginta ka tsamo ta. Ba ta da kowa sai kai. Idan ba ka dawowa kana ɗebe mata kewa ya za ta yi?  Wani ko ya dawo ɗin ma, ba shi da aiki sai danne-dannen waya. Ya ƙi kula ta. Haba don Allah Yayana, a dai dinga dubawa. Ko ba komai kula da iyali koyarwar Annabi ce. Zama tare da matarka da yaranka yana ƙara muku danƙon so da yarda a tsakaninku.

Mu haɗu a mako na gaba.