Mijina ne ya dasa min sha’awar yin takara – Halima Amadu Jabiru

“Ba zai yiwu a samu cigaba ba tare da gudunmawar mata ba” – Halima

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya

Hon. Halima Amadu Jabiru gogaggiyar ’yar siyasa ce da ta daɗe ta kuma ƙware a harkar siyasar Jihar Nasarawa da ƙasa bakiɗaya. Ta fito takarar kujerun siyasa da dama a jihar. Ta na daga cikin yan siyasa da su ka fara kafa jamiyyar PDP a jihar kafin daga baya ta canja sheka zuwa APC. A yanzu ita ce Kwamishiniyar Ma’aikatar mata da bunƙasa walwalar jama’a a Jihar Nasarawa. A tattaunawarta da wakilinmu a ofishinta da ke ma’aikatar a Lafiya, ta bayyana tarihin rayuwarta, inda ta kuma ƙalubalanci mata su shiga harkar siyasa a dama dasu don acewarta ba zai yiwu a samu ci gaba a jihar da ƙasa bakiɗaya ba tare da gudumawarsu ba. Ga yadda hirar yakasance:

Mu fara da tarihin rayuwar ki.
Sunana honorabu Halima Amadu Jabiru. Kodashike ni yar asalin garin Lafiya hedikwatar Ƙaramar Hukumar Lafiya anan Jihar Nasarawa ce. Amma an haife ni ne a garin Lokoja a shekarar 1967 a lokacin ta na Jihar Kwara, wanda yanzu shine hedikwatar Jihar Kogi. Na fara karatun firamare ɗina a ‘Holy Trinity Transfer School’ a Lokoja kafin aiki ya koma da mahaifina Jihar Kwara inda na ci gaba da karatun firamare ɗina a wajen a ‘St. Barnabas primary school’. Daga nan sai bayan wasu lokuta aiki ya sake ɗaga mahaifina zuwa Jiharmu ta Nasarawa inda na kammala karatun sakandare ɗina a ‘Government Girls Secondary school dake garin Garaku hedikwatar Ƙaramar Hukumar Garaku a Jihar nan. Daga nan na ci gaba da karatu a makarantar kimiya da fasaha ta Jihar Filato dake garin Jos inda na samu difuloma ɗina a fannin ‘accounting’. Dana kammala ne sai na ci gaba a jamiar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Bauchi a Jihar Bauchi inda na ci gaba a matakin digiri. Na kuma ci gaba da karatuna a jamiar ta Abubakar Tafawa Balewa inda na yi karatu a matakin ‘Post graduate’ duka a fannin ‘accounting’. Ni uwa ce kuma a yanzu da nake magana da kai ni ɗaliba ce, ina ci gaba da karatuna a babbar jamiar jihar nan da ke garin Keffi inda nake karatun digiri ɗina na biyu amma karon nan a fannin siyasa wato ‘political science’ a turance. Kuma kamar yadda ka sani a yan kwanakin nan ne sabon gwamnan jihar nan maigirma Injiniya Abdullahi Sule ya naɗa ni kwamishiniyar wannann ma’aikatar mata da bunqasa walwalar jama’a. Kaji kaɗan daga cikin tarihin rayuwata kenan.

Mu ji wasu daga cikin ayyukan da ki ka yi.
Na fara aiki ne da ‘Lion Bank’. Daga nan saboda kasance wata uwa sai na fuskanci wannan aikin banki yana takuramin ta yadda bana samun isheshen lokaci wa iyalaina. Hakan ya sa na bar aikin. Daga nan na dawo ina aiki da kamfanin maigidana da ake kira ‘Lafiya Engineering company’ inda na yi aiki a matsayin shugabar fannin akanta. Na kwashi kimanin shekaru 10 ina aiki da kamfanin. Ina aikin ina kuma taɓa siyasa kafin daga bisani na shiga siyasa dumu-dumu. Kuma ina ɗaya daga cikin waɗanda su ka fara kafa jamiyyar PDP a jihar nan a tsakanin shekarar 1998 zuwa 1999 inda muka yi ta gwargwarmaya a siyasance har Allah ya kaddara na fito nemar takarar kujerar mamba mai wakiltar mazabar Lafiya ta tsakiya a majalisar dokokin jihar nan a shekarar 2003. Sai dai Allah bai ƙaddara na yi nasara ba. Duk da haka ban yi kasa a gwiwa ba na sake neman kujerar a 2011 na kuma nema a 2015. Kuma duka waɗannan zaɓuka da na nema babu wanda ban samu ba. Sai dai saboda wasu dalilai da mu mata muka samu kanmu ciki inda kullum ake ganin bai dace mace ta jagoranci alumma ba. Shiyasa zaka yi mamaki a duka zaɓukan za ka ga ƙuri’u kwaya biyu ne kacal ake wuceni dasu. A wani lokaci ma ka ji wai kwaya ɗaya ne kacal aka ka da ni da shi. Zan iya tuna ma a ɗaya daga cikin zaɓukan akwai wanda da farko aka bayyana cewa munyi kunnen doki da abokin karawata. Amma maimakon a maimaita zaɓen amma sai aqarshe aka bayyana shi cewa shi ya lashe zaɓen kuma hakan ya faru ne bayan an bayyana cewa ba a qirga wasu ƙuri’una ba wai don sun lalace. To, amma a matsayita ta Musulma wace ta yarda da Allah da kuma ƙaddara ban kaucewa jamiyyata ba. Na ci gaba da kasance a jamiyyar ina yi mata aiki don a kullum na tabbata cewa idan lokaci da Allah ya ce za ka yi abu za ka yi. Daga bisani ne na yanke shawarar canja sheƙa zuwa jamiyyar APC mai ci yanzu a jihar nan bayan na lura an samu ci gaba a fannonin rayuwa daban-daban da dama a ƙarƙashin jagorancinta. Sai na ce wa kaina dama ina fito neman kujerun siyasar ne saboda in bai da tawa gudumawa ga ci gabar jihar nan mai zai sa ba zan shigo APC ayi tafiyar dani ba?. Amma kafin nan kamar yadda ka sani na yi aiki da gwamnatin PDP da ta shuɗe ta marigayi tsohon gwamnan jihar nan Aliyu Akwai Doma, Allah Ya jiƙansa. Na yi aiki a lokacin a matsayin mai taimaka masa na musamman da kuma mai ba shi shawara na musamman da sauransu kafin tsohon gwamnan jihar nan wanda yanzu sanata ne wato sanata Umaru Tanko Almakura ya ba ni muƙamin kwamishinan Ma’aikatar Filaye da tsare-tsare. Matsayi da na riƙe kenan zuwa lokacin da aka fara zaɓen daya gabata inda bayan gwamnanmu na yanzu Injiniya Abdullahi Sule ya yi nasara sai ya nadi ni kwamishiniyar wannan ma’aikatar mata da bunkasa walwalar jama’a. Kuma matsayi da nake riƙe da shi kenan a yanzu da yardar Allah.      

Akan ce iyaye makarantar farko ga yayan su. Ko za mu iya sanin abin da ki ka koya wurin na ki iyayen?
Alhamdu llillah, ka ga ni na fito ne daga babban gida. Abin da nake nufi da babban gida shi ne; na fito ne daga gidan sarauta inda za ka tarar da muhimman mutane. Ni dai a ɓangaren iyayena mu yan sarauta ne. iyayena ne ke riƙe da sarautar garin nan na Lafiya. Marigayi maimartaba Sarkin Lafiya Isah Mustapher Agwai da ya rasu kwanan nan mahaifi ne a guna. Don kakan mahaifina ya yi sarki a Lafiya wato ya fito ne daga gidan sarautar Unguwar Galadimawa wato waɗanda a yanzu suke cewa suma a sa su a jerin masu neman kujerar sarkin Lafiya wato gidan sarautar Bage kenan da ke Unguwar Galadimawa. Haka a ɓangaren mahaifina kakansa shine mai shariar gargajiya a lokacin. Duk shariar garin nan shine yake yi. Saboda haka na taso ne a gidan sarauta babba kuma hatta maigidana shi ma ɗan sarki ne don iyayensa sun yi sarauta a garin nan. Kowa kuma yasan cewa duk wanda ya taso daga babban gida dole ne ya koyi kyawawan tarbiyya musamman na girmama na-gaba, da sanin mahimmancin mutum ɗan’uwansa. Mun tashi mun san mai ya dace, da wanda bai dace ba. Ba kamar abin da ke faruwa yanzu ba. A lokacinmu iyayenmu ma ba ruwansu da mu don makwabci ma zai iya hukuntamu idan muka aikata ba daidai ba, sai dai iyayenmu suji labari su kuma yaba wa wanda ya hukunta ka. Amma yanzu idan ka kuskura ka tava ɗan wani, ka ja wa kanka babban tashin hankali. Saboda haka a taƙaice a gaskiya na koyi tarbiyya masu kyau da na ke tare da iyayena ba shakka.

Waɗanne nasarori ki ka samu a rayuwa?
Wato ni Allah ya yini mace ce da ba ta tsoro. Duk abin da na tunkara a rayuwata ba na tsoro sai na kammala shi. Zan daraja ka in kuma girmama ka, amma bana tsoronka. Siyasa nakan fito gabagaɗi in tsayawa alummata musamman marasa galihu in bi musu haƙinsu. Duk waɗannan kujerun siyasa da na bayyana maka cewa na nema duk ina yi ne don in bauta wa alummata. Kuma a kullum ina tare da su. Shiyasa da ka shigo nan ofishina ka ga jama’a da dama. Ina iya ƙoƙarina a kullun in tallafa musu iya gwargwado don na tabbata hakan shi ne babban dalilin kasancewarmu a duniyar nan. Saboda haka a taƙaice zance wannan shi ne babban nasara daga cikin ɗimbin nasarori da na cimma a rayuwata da yardar Allah, wato taimaka wa alumma akoyaushe a kuma ko wane hali.

Taura biyu ba sa taunuwa lokaci ɗaya, inji Bahaushe. Ta ya ki ke iya haɗa aiki da kuma kula da iyalanki?
Wato da farko na gode Allah don na fara siyasa ne bayan yayana sun yi girma, sun mallaki hankalinsu. Kuma ni mace ce da akoyaushe nake tsara ayukana ta yadda basa shafar harkokin gidana. A matsayina na uwa bana barin aikina ya shafi yadda nake kula da iyalaina. Don a matsayina na Musulma haƙƙi ne daya rataya a wuyana in yi duk mai yiwa wajen kula da gidana yadda addinin Musulunci ya tanadar. Shiyasa shikansa maigidana Allah ya jiƙansa da yake raye ya yi ta yaba mini a wannan ɓangare, kuma ya riƙa ƙarfafa mini gwiwa, ya kuma bani cikakken goyon baya. Yakan ce min nasan za ki iya, nasan ke wace ce. Duk abin da namiji zai yi don ƙarfafawa matarsa wannan bawan Allah ya yi mini. Ka da kayi mamaki shi ya jawomin kwaɗayin shiga siyasa. Akwai lokacin da muka tafi Umura a Saudiya inda daganan muka tafi yawo a wata ƙasa, sai wata rana ya kirani ta waya ya ce ba za ki dawo gida ba? Ga jamiyyar PDP ta buɗe ragistar mambobinta. Ina zuwa gida Nijeriya sai ya ce maza ki je ki yi ragista ayi da ke a PDP don nasan za ki iya harkar. Wallahi yadda nafara kenan. A duk lokacin da muka fita yawo da shi muna dawo wa gida sai ya ce min kin manta kina da ‘meeting ɗinki na siyasa ƙarfe kaza? Maza ki tafi ki canja kaya ki tafi ka da ki makara.

Halima tare da ahalinta

Rayuwa na tattare da ƙalubale. Waɗanne ki ke fuskata?
Babban ƙalubalan shi ne; yadda ba a qarfafa ko bai wa mata damar da ya kamata don su ma su fito neman kujerun siyasa a jihar nan da ƙasa bakiɗaya, kasancewa a yanzu siyasa ta koma ta kuɗi. Ya kamata ace an tsara tsarin ta yadda ba mata kawai ba duk wanda ya cancanta ya fito takarar kowanne kujerar siyasa a ƙasar nan a bashi damar ko ya na da kuɗi ko bashi da shi. Na tabbata ta haka ne alumma za su iya zaɓe shugabanninsu nagari. Ƙalubale na biyu kuma shi ne; yadda wasu maza ke ɗaukar mata cewa ba za su iya jagoranci alumma a siyasance ba. Kodashike ba na ganin haka a matsayin ƙalubale shiyasa duk da na sha wuya sosai a gwargwamayar siyasa da nake yi duk da haka ban yi ƙasa a gwiwa ba na ci gaba kuma ina koyon abubuwa da dama ta harkar, don akoyaushe inaso ne in kasance abar koyi da misali ga sauran ‘yan’uwana mata musamman waɗanda ke tasowa.

Ko akwai shawarar da za ki bawa mata da matasa?
Shawarar ita ce; kamar kullum bai kamata a ce ana harkokin siyasa da mulki da sauransu ban da mu mata. Idan ba a yi damu mata ta yaya za a san matsalolinmu. Kuma ba zai yiwu a samu cigaba a ƙasar nan ba tare da gudumawarmu mata ba. Kuma mata mu ne muke da yawan ƙuri’u da hakan ya ba mu damar fito da duk wanda mukeso ya shugabancemu. Saboda haka dole ne mu fito ƙwanmu da ƙwarƙwata mu riƙa fafatawa a harkokin siyasa da sauransu don bada tamu gudumawa a wannan ɓangare don bamu damar ci gaba da more ribobin dimokaraɗiyya.

Ƙasashe nawa ki ka ziyarta?
A gaskiya kasancewata Musulma na fi tafiya aikin ibada ne a Ƙasar Saudiyya. A duk lokaci da na samu hutu nakan ziyarci ƙasar ce don in gudanar da ibada ga mahalicina, in gode masa a kan abubuwa da dama da ya yi wa iyalaina da ni kaina a rayuwata. Sauran ƙasashe da nake sha’awar tafiya kuma sun haɗa da Faransa da Dubai da London da Amsterdam da sauransu. Amma nafi tafiya ƙasashe biyun ne wato Saudiya da Dubai. Sauran ƙasashen da na bayyana ayyuka ne suke kai ni.

Tufafin da ki ka fi sha’awa?
Ni dai idan ka lura irin yadda wasu mata ke fita irin na turawa ka ga suna sauye fatar jikinsu da sauransu baya game ni. Ni inason tufafi ne irin namu na matan Arewa. Don ni yar Arewa ce, uwa kuma musulma. Dole ne in riƙa sa tufafi da za su tsare min mutunci akoyaushe kamar dai yadda addinin Musulunci ya tsara.

Mun gode da lokacin ki.
Ni ma na gode.