Zaratan marubuta biyar na duniya

Daga AISHA ASAS

Rubutu daɗaɗɗen abu ne da ya kwashe shekaru masu yawa ya na gudana, wanda hakan ya sanya ake samun saɓani a wurin ƙididdige shekarun sa, domin a duk lokacin da akayi matsaya ga shekarar da aka fara rubutu sai a samu wata hujja da ta tabbatar da rubutu kafin lokacin, don haka shekarun rubutu a duniya sun kasu da dama.

Rubutu na ɗaya daga cikin ayyukan da ba su cika mutuwa ba, musamman idan an inganta shi. Marubuci na cikin hallitun da Allah ya bawa baiwar hasashen gaba, kamar wasu rubuce-rubuce, da waqe da aka rubutu shekaru masu yawa da ke yawo a yanzu, wanda idan ka na karantasu, za ka ji tamkar a wannan ƙarni aka fitar da su. saboda ababen da su ka ƙunsa wanda ba maraba da halin da muke ciki.

A Arewancin Nijeriya, da yawa a marubuta ba su san darajar baiwar da aka basu ba, hakan ya sanya ko kaɗan basa tauna abin da su ke rubutawa. Ba sa tunanin inda rubutun na su zai kai, ko shekarun da zai yi ya na rayuwa a doron ƙasa.

Sun mayar da rubutu gasa tsakaninsu, ko wata hanyar samun kuɗi kawai. Wasu daga cikin marubuta kuwa neman suna kan rufe masu ido har su ka sa fahimtar ma’anar baiwar, hakan kan sa basa damuwa da dacewar rubutun da su ke yi matuqar za su birge makarantansu. Dalilin kenan da ya kawo yawaitar marubutan batsa, domin zamani ya zo da batsa ta zama abin muradin mutane, har wasu kan kauce wa karanta rubutun marubuta da ba sa batsa a ciki.

Ko wannan zai iya zama dalilin da zai sa marubuci canza sheƙa, daga irin salon da ya fara rubutunsa a baya zuwa wani don kawai ya tafi da zamani? Shin ya za ki ji ya ke marubuciya, a lokacin da ɗa ko jikanki ya ci karo da littafin da ki ka yi a shekarun ƙurciya, wanda yake cike da kalaman baɗalla? Ta ya za ki iya yi ma sa nasiha ko faɗan gyara kayanka?

Wasu marubutan kuwa gaggawa ce ke hanasu cin moriyar rubutu a gaba, domin basa iya tsayawa su tabbatar da ingancin abin da su ka rubutu kafin su fitar da su, hakan kan hana tasirin baiwarsu. Ɗaya daga cikin dalilan da ke sa idan ka ci karo da rubutun da ya birgeka, yanayin rubutun da yadda yake ɗauke da kura-kurai ba za su hana ka daraja rubutun, ko bashi wani matsayi.

Hakan na cikin dalilan da su ka hana ‘yan Arewa cin moriyar rubutu tare da samun kujerar zama a muhallin marubuta da ake ji da su a duniya. Ba wai baiwar ce babu ba, rashin amfani da baiwar yadda ya kamata ne tare da sa son rai.

A wani bincike da na ci karo dashi a kwanakin baya ya tabbatar da cewa; Arewa ta fi ko ina yawan marubuta a garurukan duniya. Sai dai sun zama taron tsintsiya ba shara ne ya sa duniyar bata ɗauki amon bajintar su ba.

Da yawa a marubuta su kan ɗaura laifin gazawar su kan gwamnati, a cewar su ba su samu tallafin gwamnati ba shi yasa basu kai tudun shahara ba. Sai dai a na wa gani rubutu shi ke fitar da kansa, kuma ingancinsa ne babban jigon da ka iya kai ka ga shahara.

Kaso mai yawa na marubutan da su ka shahara, duniya ta san da su, za ka samu ba sa hanzari wurin fitar da littafi, su kan natsu, su ɗauki lokaci, kafin ka ji sun fitar da littafi. Wannan shine rubutu, domin zai yi wahala ka tarar da kura-kurai, ko wani abin takaici a littafin, saboda anbi duk wata hanya da za ta ingantashi.

Idan da marubutan mu za su cire son rai, su nemi sani da zai wanke masu baiwarsu, su laƙance bincike, tare da neman ilimin harshen Hausa, su cire gaggawa tare da kallon abin da wasu marubutun su ka yi na daga adadin littafai, da tabbas duniya za ta san da zaman marubutan mu. Za mu shiga jerin marubutan duniya, domin duk da cewa Hausa ba ta da ƙasa, kamar sauran wasu yaren duniya, ta na da mutane ma su magana da ita da su ka kai adadin yawan wata ƙasa, don haka ba zai zama matsala ba wurin shigar marubutan ta jerin marubutan duniya ba.

Ka da in ja ku da nisa, domin wannan shafin na wannan sati zai yi magana ne kan zaƙaƙuran marubutan da duniya ta ke alfahari da su, don haka ku biyo mu:

Lev Nikolayevich Tolstoy:
Lev Nikolayevich Tolstoy wanda aka fi sani da Leo Tolstoy, ya kasance marubuci da ya shahara a rubutu na labarai da su ka fi kama da gaskiya. Mutumin Rasha ne da ake ji da shi a fannin rubutu, a hasashe za a iya kiransa marubuci da duniya ta fi ɗagawa a rubutu da ya fi kama da rayuwar gaske, wata kila hakan na da nasaba da zamewar sa masani kuma gwani wurin karantar rayuwa, tare da amfani da ita wurin isar da saƙo ta hanyar alƙalamin sa. Yayin da wasu ke kallon wasu marubuta a matsayin marubutan nishaɗi da ke nutso da su suna ninkaya cikin duniyar mafarki, suna kallon Leo a matsayin marubucin rayuwar da ta ke gudana, hakan ne ya bambanta shi da saura, kuma ya bashi matsayi na musamman a zukatan makarantan sa, kamar dai yadda wani marubuci ɗan Rasha Isaak Babel ya faɗa “idan duniya za ta yi rubutu kan kanta, to tabbas za ta yi rubutu ne irin na Leo Tolstoy.”

Leo Tolstoy

Ya kasance ɗaya daga cikin zavavvu da a ka ware don zaɓar gwani a gasar fidda gwani ta ‘novel price’ a vangaren addabi. Tun daga shekara ta 1902 suna sa ke fitowa a jerin zaɓaɓɓun har shekara ta 1906.

An haifi Leo a 9 ga watan Satumba 1828, a Yesnaya Polyana ta Ƙasar Rasha. ya fara rubutu a shekarun ƙurciya wanda littafinsa na farko ya kasance akan abin da rayuwar ƙurciya ta koya ma sa. Shi dai Leo ya kasance maraya tun ya na da shekara biyu a duniya mamarsa ta mutu, yayin da baban sa ya bi bayan ta kafin ya cika shekara goma da haihuwa. Kakar sa ta bi bayan baban sa watani 11 bayan mutuwar sa.

Ya rubuta littafin sa na farko a shekara ta 1852 wanda ya ƙaga dai-dai da kwatankwacin rayuwarshi ta ƙurci, inda ya ɓoye kan sa a wannan littafin.
Fitattu da su ka fi saura daga cikin littafan sa su ne; ‘War and peace’ wanda ya rubuta a shekara ta 1865 zuwa shekara ta 1869, da kuma ‘Anna Karenina’ a shekara ta 1875 zuwa 1977.

Leo ya mutu a ranar 20 ga watan Nuwamba shekara ta 1910, a garin Lev Tolstoy. Ya mutu ya na da shekara 82. 

Jane Austen:
Baturiyar Ƙasar Burtaniya, marubuciya ce da ta fi ƙarfi a rubutun zube, duk da cewa tayi rubuce-rubuce da dama da za a iya kiranta da marubuciya da ta tavo ko wane ɓangare cikin adabi, sai dai rubutun zube ne ya fitar da ita duniya ta san da ita, ta sanadiyyar littafan ta guda shida. Akwai ‘Pride and prejudice’ wanda ta rubuta a shekara ta 1813, ‘sence and sencibility’ a shekara ta 1811, ‘Mansfield park’ a shekara ta 1814, ‘Emma’ a shekara ta 1815. ‘persuasion’ a shekara ta 1817. Northhanger Abbey a shekara ta 1817.

Jane Austen


Duk da cewa Jane ta yi suna, kuma ta shahara, littafai huɗu daga cikin littafan ta ne kawai ta samu ganin fitowarsu kafin mutuwar ta, biyu ragowan littafanta da su ka yi fice sun fito ne bayan mutuwarta, yayin da sauran rubuce-rubucenta aka harhaɗa su tare da tsara su zuwa ga mahaɗa ɗaya da aka yi wa tsarin mujalladi, inda ya fito a mujalladi na ɗaya har zuwa na uku, wato volumes a turance .

Shin wace ce Jane Austen?
An haifi Jane 16 ga watan Disamba shekara ta 1775, a ƙauyen Stevenson a garin Hampshire da ke Ƙasar Ingila. Marubuciya ce ta farko da ta fara fito da sallo na zamanantar da rayuwar talaka ta hanyar nuna muhimmancin mu’amallar sa da mai arziki.

Marubuciyar turancin Jane Austen kan yi amfani da baiwar da ta ke da wurin tsara rayuwa ta matsakaitan mutane inda ta ke amfani da qarfin alƙalami wurin ganin ya isar da saqo na bajinta da zai canza tunanin mutane.

Yanayin rubutun nata za mu ce ya fi ta’allaƙa ne kan zamantakewar aure da kuma soyayya, wanda hakan kan ba wa makaranta littafan ta mamaki, ganin cewa Jane bata tava aure ba, kuma sai ga shi ta na rubuta labarai da ke tava zukatan mutane, tare da sanya ababen da su ke wakana a irin rayuwar ta zahiri, kuma daga ƙarshe taba shi ƙarshe da zai kasance muradin makaranci. Wannan dalilin ne yasa mutane zargin ko Jane ta shiga wani tasgaro na soyayya da ya sanyata ƙoƙarin bayyana ƙuncinta ta hanyar alƙalamin ta.

Sai dai wannan zargin bai samu amsar da za ta tabbatar da shi, ko zaunar da shi a muhallin sa na zargi kawai ba, dalili, Jane a farkon rubutun ta ta na basaja, ma’ana bata bayyana wa duniya kan ta a matsayin marubuciya, don ta fitar da dukka littafan da ta yi a raye ba tare da ta bayyana asalin sunanta ba. Duniya ta san Jane Austen a matsayin marubuciyar da ta rubuta littafai huɗu a baya ta sanadiyyar ɗaya daga cikin ‘yan’uwanta maza mai suna Henry wanda ke tsakanin ta da masu buga mata littafi, don haka shi ne ya fara fitar da sunan ta a littafin ta da ya fara fita bayan mutuwarta mai suna ‘Northhanger Abbey’.

Don haka bayan mutuwar ta ‘yan’uwanta su ka mutunta muradin ta na ɓoye sirrin rayuwar ta ga duniya. Musanman ma ‘yar’uwar ta cassandre da a ka tabbatar sun fi shaƙuwa da ita fiye da sauran ‘yan’uwanta 8. Wadda su ka kasance su biyu kawai mata, yayin da ragowan shida duk maza ne.

Na san mai karatu zai yi wa kan sa tambayar me yasa ta ɓoye kan ta? A wancan lokaci mata suna cikin wani takunkumi da ya haramta masu hawa matakalan mafarkin su, abin da ake buƙatar gani ga ko wace mace shi ne; ta yi auren ƙwarai, inda za ta samu hutu da biyan buqatun yau da kullum.

Jane ta mutu a shekara ta 1817, 18 ga watan Yuni, a ƙauyen Winchester da ke cikin garin Hamshire.Ta kasance ta na rubuta wani littafin ta mai suna ‘persuasion’ a lokacin da ciwon ta ke tsananta, hakan ya sa ta kasa ƙarasa wa saboda ciwon da ya ci ƙarfin ta, wanda ya yi silar ajalinta.

Za mu ci gaba…