Rashin sha’awar iyali da dalilansu (3)

Daga BILKISU YUSUF ALI

Cigaba daga makon jiya

A sati biyun da suka gabata duk muna yin bayani ne kan abin da ke hana sha’awa ko ya katse ta bayan a baya ana zaune lafiya babu wannan damuwar, kuma ana ƙaunar juna da son kasancewa tare. Mun kawo abin da ke haifar da wannan matsaloli waɗanda muka haɗe su a ƙarƙashin matsaloli da zamantakewa ke haifarwa na yau da kullum. Sai dai kuma tun a farko mun ce matsalolin sun kasu ne gida biyu; wato matsalolin da yanayin rayuwa da zamantakewa ya haifar, sai kuma kashi na biyu wanda larura ko rashin lafiya ke haifarwa har a kai ga an rasa sha’awa tsakanin iyali.

Cututtuka da daman gaske kan shafi matsalar sha’awa har ya zamana tun ana fama da kaɗan-kaɗan har ya kai ga sha’awar ta fita gaba ɗaya. Akwai matsala da larura ta rashin lafiya akwai kuma wadda ta shaiɗanu ce wanda wannan wani fage ne daban wanda masana wannan suna nan. Ni zan yi bayani ne kan matsalar rashin lafiya da wani ciwo ya haddasa. Makarin wannan matsala kuwa shi ne neman magani.

A ɓangaren maza da mata kusan dukkan matsalolin guda ɗaya ne akwai:

*Ciwon sanyi. Shi ciwon sanyi yana hana sha’awa kwata-kwata. Ciwon sanyin nan kala-kala ne, akwai sanyi na jiki kuma akwai na mara. ko irin wanda ake ɗauka yayin amfani da banɗaki marar tsafta ko a jikin abokin mu’amala da sauran nau’ikan sanyi da ke sa zubar farin ruwa ko bushewar gaba ko zafi yayin kusantar juna. Kowanne yana da tasiri a jikin ɗan’adam da mu’amala ta aure. Wannan yana hana sha’awa da gamsar da abokin zama.

*Ciwon basur shi ma yana hana sha’awa wanda ya kamata mutane su kula da abunuwan da suke ci saboda yawanci matsalar kan taso daga ci ma da yanayin tsarin rayuwa.

*Ciwon damuwa ko fargaba shi ma yana ɗauke sha’awa.

*Ciwon suga yana hana sha’awa kuma ko da sha’awar ta samu to za a ga namijin ba shi da cikakkiyar lafiyar kusantar iyalin.

*Yin istisma’i (amfani da hannu) shi ma yana hana sha’awa. Haka amfani da wasu abubuwa da mata kan yi don biya wa kansu buƙata shi ma yana kassara sha’awa.

*Ga matar da aka taɓa yi mata fyaɗe musammam in har ba ta sami kulawar jami’an lafiya ba shi ma yana haifar da matsaloli ciki kuwa har da akwai wannan matsala ta rashin sha’awa.

*Yawan amfani da magunguna musamman na mata barkatai marassa inganci haka su ma mazan akwai waɗanda suke mayar da magunguna musamman na maza wata ƙa’ida kullum sai sun sha , to wannan kan haifar da matsaloli musamman na ɗaukewar sha’awa ga kowanne ɓangare.

Waɗannan su ne kaɗan daga cikin matsalolin da suke hana mata da maza sha’awar iyalinsu.

Ga mai tambaya ko ƙarin bayani yana iya tuntuɓar wannan layin amma tes kawai ko ta whatsup 08039475191 ko a shafina na facebook Bilkisu Yusuf Ali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *