Kotu ta ɗaure ɗan Abdulrashid Maina, Fisal shekaru 14 a kurkuku

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ƙarƙashin Alƙali Abang Okon, ta yanke wa ɗan gidan Abdulrashid Maina, wato Faisal hukuncin ɗauri na shekara 14 a gidan yari. Tare kuma da umurtarsa da ya maido da kuɗi Naira miliyan 58 da dubu 100 ga Gwamnatin Tarayya.

A wannan Alhamis ɗin Kotun ta yanke wannan hukuncin, inda ta tuhumi Faisal Maina da laifuka uku da suka haɗa da almundahana da safarar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba, kuma an yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyar ne a kan ko wane laifi.

Lauyan gwamnati da ke wakiltar hukumar EFCC da ta shigar da ƙarar Faisal, Muhammed Abubakar ya bayyana cewa wanda ake tuhumar ya tsere zuwa ƙasar Amurka inda ya fice daga Nijeriya ta ƙasar Nijar duk da cewa fasfot ɗinsa na Nijeriya da Amurka na hannun kotu.

Abubakar ya ƙara da cewa, an yi ƙoƙarin kamo Faisal daga ƙasar Amurka ta bin tsarin dokar ƙasa da ƙasa amma hakan ya ci tura.

Sai dai lauyan Faisal Maina, Anayo Adibe, ya musanta kalaman lauyan EFCC inda ya ce ‘yan sanda sun kama wanda yake kare wa ne a garin Sakkwato, ya kuma buƙaci kotun ta bada damar binciken gano inda Faisal Maina yake.