Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministar ƙwadago da Jinƙai ta ƙasar Cuba, Marta Feito Cabrera, ta sauka daga muƙaminta bayan ta ce babu mabarata a ƙasar, sai dai masu ƙaryar kasancewa mabarata.
Fadar Shugaban ƙasar a ranar Laraba ta sanar da cewa Ministar ta amsa kuskurenta sannan ta miƙa takardar ajiye aiki kan abin da ta kira “nuna rashin tausayi da rashin ƙwarewa a kan batun da yake da tasiri a siyasance a ƙasar.
Labarin dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan Ministar ta yi kalaman a gaban ’yan kwamitin majalisar ƙasar a kan talauci a ƙasar wacce tsibiri ce.
Marta dai ta ce, “Mun ga mutane, waɗanda a Zahiri mabarata ne, amma idan ka kalli hannunsu, ka duba tufar da ke jikinsu, za ka ga sun yi ɓad-da-bami a matsayin mabarata, amma ba mabarata ba ne.
“A Cuba, babu mabarata,” inji ta.
Ta kuma ce mutanen da ke wanke wa masu motoci gilashin motocinsu a kan titi suna rayuwa mai sauƙi, kuma sukan yi amfani da abin da suka samu wajen sayen barasa.
Nan take kalaman nata dai suka karaɗe gari, musamman a shafukan sada zumunta, inda aka riƙa kiraye-kirayen ta ajiye muƙaminta.
ƙasar Cuba dai na cikin mawuyacin halin matsin tattalin arziki a ’yan shekarun nan.
Hatta Shugaban ƙasar, Miguel Diaz-Canel sai da ya soki lamirinta.
ƙasar dai ta shiga ƙangi ne tun bayan wani takunkumin tattalin arziki da Amurka ta ƙaƙaba mata a shekarar 1960, lokacin da Fidel Castro ya jagoranci juyin juya hali a ƙasar.
