Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mamallakin rukunin kamfanonin ɗangote, Aliko ɗangote, ya nuna shakkunsa kan yuwuwar iya farfaɗo da matatun man Nijeriya har su dawo aiki kamar yadda ya kamata.
ɗangote ya bayyana hakan a yayin da yake magana da ɗaliban makarantar koyon kasuwanci ta jihar Legas a ranar Alhamis a yayin rangadi da su a matatar mansa da ke Lekki a jihar.
Ya ce, matatar gwamnatin tarayyar wacce ke ƙarƙashin kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC Ltd), ta laƙume kuɗin Nijeriya Naira biliyan 18 ba tare da ganin wani sakamako ba.
Ya kuma ƙara da cewa ya gina matatar mansa mai cin ganga 650,000 ne bayan da ya nemi gwamnatin marigayi tsohon shugaban ƙasa, Umar Yar’adua, ta siyar masa da matatun amma ta ƙi.
“Matatar man da muka siya a baya mallakin Nijeriya na samar da kaso 22% na man fetur. A watan Janairun 2007 muka siyi matatun. Amma tilas muka sake dawowa da gwamnati matatun bayan an samu sauyin gwamnati.”
“Kuma shuugaban kamfanin man fetur na wancan lokacin ne ya ba Yar’adua tabbacin cewa matatun za su iya cigaba da aiki. Sun kuma ce ai an ba mu matatun ne a matsayin ladan gafe. Kuma izuwa yanzu sun kashe wa matatun Naira biliyan 18 duk da haka ba su farfaɗo ba. Gaskiya ba na tunanin matatun nan za su farfaɗo har su cigaba da aiki,” inji ɗangote.
Ya ce, yanayin kula da matatun man fetur ɗin kamar “ƙoƙarin sabunta motar da aka ƙera ce shekaru 40 da suka wuce ce a lokacin da fasahar da komai da komai ya canja.”
“Ko da ka canja inji, gangar jikin ba za ta ɗauke sabuwar fasahar da ke tattare da injin ba,” ya bayyana.
Shugaban kamfanin NNPC, Bayo Ojulari, ya bayyana makamacin wannan ra’ayi na ɗangote yana mai bayyana yuwuwar kamfanin na sayar da matatun man saboda wahalar da ake sha wajen sabunta su.
A yayin da yake magana da Bloomberg a ranar Alhamis a lokacin taro na ƙungiyar ƙasashe masu arziƙin man fetur karo na 9, Mista Ojulari ya ce a yanzu haka ana nan ana nazarin matatun NNPC kuma ana sa ran kammala wannan nazari kafin ƙarshen shekarar nan.
“Muna sake nazarin matatun man fetur ɗinmu. Muna sa ran kafin ƙarshen shekara za mu kammala wannan nazarin. Wannan nazari shi ne zai kawo sauyi ta watta fuska,” a cewarsa.
A yayin da aka yi masa tambaya kan sayar da matatun man fetur, Mista Ojulari, ya ce, “Abin da muke cewa shi ne akwai wannan maganar. Za mu duba dukkan ɓangarorin, amma hakan ya dogara ne da sakamakon nazarin da muka yi.”
A watan Nuwambar shekarar da ta gabata, fadar shugaban ƙasa ta bayyana shirinta na cefanar da matatun man Nijeriya.
Nijeriya na da matatun man fetur guda biyu: Matatar man Fatakwal da matatar Ribas wacce ta haɗu ta samar da kamfanin matatar Fatakwal (PHRC) waɗanda ke iya tace gangar mai 210,000 a kowacce rana.
Sai kuma matatar man Kaduna (KRPC) wacce ke iya tace gangar mai 110,000 a kowacce rana da kuma matatar man Warri (WRPC) da ke iya tace gangar mai 125,000.
Dukkan matatun man fetur ɗin za su iya ta ce gangar mai 445,000 a kowacce rana.
Sai dai duk da wannan kuɗaɗe da ake kashewa, matatun man fetur ɗin na fuskantar ƙalubale wanda hakan ke nuna yadda matatun suka gaza.
Hatta matatar man Warri wanda aka sake buɗewa a watan Disambar 2024 an sake rufe ta a watan Janairu saboda dalilai na kare lafiya. A watan Mayu ne, kamfanin NNPC ya sanar da rufe matatar mai ta Fatakwal.
