Miyetti Allah ta yi allawadai da kisan Fulani 43 a Kebbi 

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta ƙasa (MACBAN), ta yi allawadai da kisan Fulani makiyaya 43 a daga yankunan jihohin Kebbi da Neja. 

Wannan bayani yana ƙunshe ne a wata takarda mai ɗauke da sa hannun sakataren ƙungiyar na ƙasa Alhaji Bello Aliyu Gotomo ya fitar a Hedikwatar ƙungiyar dake Abuja ranar Alhamis ɗin da ta gabata.

Takardar ta ce ƙungiyar ta Miyetti Allah ta Nijeriya (MACBAN) ta yi Allah wadai da hare-haren da aka kai ba tare da wani dalili ba, da kuma kisan mutane 43 daga cikin makiyaya masu zaman lafiya da ‘yan sa-kai masu kiran kansu “Yan Sakai” suka aikata cikin ‘yan makonnin da suka gabata.

Takardar ta nuna cewa waɗansu gungun mutane da ake sa ran ‘yan sa kai daga ƙananan hukumomin Arewa da Bunza sun yi ta kashe-kashe da ƙona bukkokin makiyaya a yankunan su musamman a gundumomin Bui ta a ƙaramar hukumar Arewa da kuma Tilli da Zogirma daga ƙaramar hukumar mulki ta Bunza inda a nan kaɗai an kashe fulani 37 da suka haɗa da maza da mata da kananan yara kuma waɗansu da dama sun jikkata yayin da  har yanzu ba a san inda waɗansu suke ba, hakazalika an ƙone sama da gidaje 200.

Takardar ta cigaba da bayyana cewa.lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Argungu a ranar 24 ga Oktoba, sai wanda ya faru a Bunza a ranar 25, sannan na Bui ya faru a ranar 26 ga Oktoba. Wannan mummunan aiki yana nuna wani shiri na ƙoƙarin tarwatsa makiyaya daga matsugunansu a wannan yanki na jihar.

ƙungiyar ta bayyana cewa matsalar tsaro da ke addabar yankunan karkara a faɗin ƙasar nan na buƙatar gaggawar kulawar gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi. 

Ta kuma yi kira ga hukumomin da su kawo musu agajin gaggawa tare da ɗaukar matakin ladabtarwa ga duk wanda ya taka doka.

By ukarofi