Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da ƙarin kuɗin tsaro ga fasinjojin jiragen ƙetare da ke shiga ko fita daga ƙasar, wanda zai fara aiki daga 1 ga Disamba, 2025.
Wannan sabon kuɗi zai ƙara Dala 11.5 a kowace tikitin jirgi, yana mai ɗaga jimillar kuɗin tsaro zuwa Dala 31.50 ga kowane fasinja.
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta ƙasa (NCAA) ta bayyana cewa wannan kuɗin zai riƙa shiga ne kai tsaye cikin tikiti tun daga ranar da tsarin ya fara aiki.
Sabon kuɗin na cikin tsarin Advance Passenger Information System (APIS), tsarin bayanan fasinjoji tun daga filin jirgi kafin isa ko tafiya. Wannan tsari zai bai wa hukumomi damar samun bayanai tun kafin fasinjoji su isa ƙasar, tare da taimakawa wajen gano barazana da saurin tantance bayanai a filayen jirgi.
A cewar NCAA, kucin da za a tara, kimanin dala miliyan 46 a shekara, za su taimaka wajen gina tsarin bayanai na zamani, na haɗin gwiwa da Hukumar Shige da Fice (NIS), wanda zai tafiyar da aikin tsaro na tsawon shekaru 20.
