Kotun ɗa’ar Ma’aikata ta bankaɗo ƙarairayin wasu manyan jami’an gwamnati

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar ɗa’ar Ma’aikata (CCB) ta bayyana cewa ta gano wasu bambance-bambance da ake zargi da rashin daidaito a cikin takardun bayyana kadarori na ministoci, manyan sakatarori da wasu manyan jami’an gwamnati.

A wata sanarwa da Daraktan Harkokin Musamman na hukumar, Moses Atolagbe, ya fitar a madadin shugaban CCB, Abdullahi Bello, hukumar ta ce sabon sashen bincike da ta kafa — Financial Investigation and Fraud Analysis Unit (FIFAU) — ya tantance sama da takardun bayyanar dukiya 500.

A cewar Bello, binciken ya riga ya tabbatar da bayanan kadarorin: Ministoci 9, Manyan Sakatarori 43 da Daraktoci na Tarayya 40.

Hakan, inji shi, hanya ce ta ƙarfafa gaskiya, adalci da ingantaccen tsarin kulawa da dukiyar gwamnati.

“Binciken ya gano wasu bambance-bambancen bayanai da za su taimaka wajen ɗaukar matakin ladabtarwa,” inji sanarwar.

Bello, wanda ya hau kujerar shugaban CCB a ranar 23 ga Oktoba, 2024, ya ce hukumar ta, ƙaddamar da tsarin yin rijistar bayyanar dukiya ta yanar gizo.

Ya ƙara jaddada manufar CCB da taken: “Bayyana ko a kwace” — Declare or Forfeit.

Bello ya gargaɗi dukkan ma’aikatan gwamnati da su bayyana kadarorinsu yadda dokar ta tanada, kana su nisanci duk wata ɗabi’ar cin hanci da rashin gaskiya.

By ukarofi