
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar ƴan fim ta Ƙasa, MOPPAN, ta yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano bisa ƙoƙarinsa na ɗaukar ɗawainiyar rashin lafiyar Hajiya Halisa Muhammad.
Halisa Muhammad, mamba ce ta masana’antar finafinan Kannywood kuma tsohuwar jaruma, wadda ke fama da cutar daji.
Shugaban MOPPAN, Malam Mai-Kuɗi ya bayyana hakan a wata takarda da Kakakin ƙungiyar, Ibrahim Amarawa ya fitar, inda ya ce hakan ya nuna yadda gwamnan ya damu da mutanensa da ma mambobin Kannywood.
Ya kuma ce za su cigaba da bai wa Gwamantin Kano cikakken goyon baya ga ayyukanta da kuma ƙoƙarin kawo cigaba a masana’antar Kannywood musamman a jihar.
