Kotun Ƙoli ta tabbatar da na hannun daman Wike a matsayin halastaccen Sakataren PDP na Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kotun Ƙoli ta tabbatar da Samuel Anyanwu, wanda na hannun dama ne ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, a matsayin halastaccen Sakataren jami’yyar PDP na Ƙasa.

A wani hukunci na tawagar alƙalai biyar, kotun ta ce lamuran da suka shafi shugabanci ko zama mamba, abubuwa ne na cikin gida ba waɗanda kotu za ta tsoma baki aciki ba.

Da haka ne kotun ta ture hukuncin Babbar Kotun Tarayya ta Jihar Enugu, wanda aka yi a ranar 20 ga watan Disambar 2024 na tabbatar da cire Anyanwu daga muƙamin, inda ta ce kotun ba ta da hurumin yin hukunci kan ƙarar.

A Disambar 2024 ne Kotun Ɗaukaka ƙara ta yi hukuncin cewa Ude-Okoye shi ne wanda zai maye gurbin Anyanwu a muƙamin.

Kasancewar matsalar ta cikin gida ce, Kotun Ƙolin ta yi watsi da hukuncin ta Ɗaukaka ƙarar duba da yadda Anyanwu ya tsaya wajen kare kujerarsa a jami’yyar.

By Babaji