Daga USMAN KAROFI
Gwamnatin Jihar Kano ta miƙa jajenta ga ‘yan kasuwar Dakata bisa iftila’in gobara da ta laƙume dukiyoyin da darajarsu ta kai ɗaruruwan miliyoyin naira. Wannan jajen ya fito ne yayin ziyarar jaje da wata tawaga daga Gwamnatin Jihar Kano ta kai ƙarƙashin jagorancin kwamishinan kasuwanci da zuba jari, Alhaji Shehu Wada Sagagi, tare da rakiyar kwamishinan labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya; mai bai wa gwamna Slshawara kan harkokin gudanarwa, Akibu Murtala Isa da kuma darakta janar na hukumar ƙananan masana’antu ta Jihar Kano (Kano State Small-Scale Industries), Alhaji Mansur Isa.
Tawagar ta zagaya kasuwar domin tantance irin ɓarnar da aka yi da kuma ganin irin kayan da suka ƙone ƙurmus, tare da tabbatar da cewa za a samar da tallafi ga waɗanda abin ya shafa ta hannun hukumar raya masana’antu da ƙananan sana’o’i (KSMIDAN).
Da yake jawabi yayin ziyarar, kwamishinan kasuwanci da zuba jari, Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya tabbatar wa da ‘yan kasuwar cewa gwamnatin Jihar Kano za ta yi duk mai yiwuwa don tallafa musu, tare da rage raɗaɗin asarar da suka yi. Ya bayyana cewa ko da yake ba za a iya mayar da dukkan abin da aka rasa ba, amma gwamnati za ta samar da tallafi domin taimaka musu a wannan mawuyacin lokaci. Haka zalika, ya sanar da cewa gwamnati na shirin samar da wutar lantarki a kasuwar domin rage dogaro da wutar KEDCO, wanda hakan zai taimaka wajen rage kuɗin gudanar da sana’o’in ƙanana a yankin da ma faɗin jihar, tare da kira ga ‘yan kasuwa da su rungumi tsarin inshorar Musulunci domin kare dukiyoyinsu daga haɗarin gobara da makamantansu.
A nasa ɓangaren, Shugaban Ƙungiyar masana’antu da ƙananan sana’o’i na Dakata, Alhaji Zulkifilu Alasan Umar, ya nuna matuƙar godiyarsa ga gwamnatin bisa irin goyon bayan da ta nuna, yana mai tabbatar da cewa za su aiwatar da tsarin inshorar Musulunci domin kare dukiyoyin ‘yan kasuwa daga irin wannan iftila’i a nan gaba. Ya yaba da matakin gwamnati na tallafawa masana’antu na cikin gida, yana mai cewa hakan yana nuna jajircewar gwamnatin wajen ƙarfafa da bunƙasar sana’o’in ƙanana, tare da farfaɗo da tattalin arzikin ‘yan kasuwar da iftilain ya shafa.
