Morocco za ta fara jigilar jiragen sama zuwa Isra’ila

Kamfanin Jiragen sama na Ƙasar Morocco, ‘Royal Air Maroc’ (RAM) sun sanar da cewa za su fara jigilan matafiya ta jiragen sama zuwa Isra’ila, shekara ɗaya bayan da qasashen biyu suka maido da ɗasawa.

Ana sa ran fara jigilan fasinja tsakanin Casablanka da Tel Aviv ranar 12 da watan gobe, kwanaki biyu bayan cika shekara ɗaya da maido da zumunci tsakanin ƙasashen biyu karkashin su.

A cewar kamfanin jiragen saman, za su riƙa jigila sau uku cikin mako ɗaya, kafin a samu jigila sau uku a mako.

Tun shekara ta 1993 Morocco da Isra’ila suka ƙulla zumunci, amman kuma Morocco ta janye sakamakon rikicin intifada na Palestinawa a shekara ta 2000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *