Lokaci ya ƙure wa duniya kan samun kariya daga sauyin yanayi

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi iƙirarin cewa alƙawarin Indiya yayin taron yanayi na COP26 a Glasgow babban abun maraba ne a ƙoƙarin da ake na yaqi da ɗumamar yanayi dai dai lokacin da illolinta suka fara yi wa duniya barazana.

Alƙaluman da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar ya yi maraba da matakin Indiya na daina fitar da sinadarin na Carbon nan da shekarar 2070, wanda ta ce zai taimaka wajen rage ƙaruwar zafin da duniya ke gani.

Shirin muhalli na Majalisar Ɗinkin Duniya UNEP ya ce matakin ƙasashen na ƙayyadaddun gudunmawarsu ta fuskar kimiyya fasaha da kuma tattalin arziki ya ƙara yawan zafin da Duniya ke gani da maki 2.7 wanda ke matsayin babbar barazana ga halittun ban ƙasa.

A cewar UNEP, akwai buƙatar rage zafin da Duniya ke gani zuwa maki 1.5 don cimma matsayar da aka qulla ƙarƙashin yarjejeniyar yanayi ta Paris.

Shirin na UNEP ya koka da cewa ko da ƙasashen sun cika alƙawurran da suka dauka yayin taron Glasgow, akwai yiwuwar matakin da aka kai wajen gurɓata muhalli ya yi tasiri ga Duniya idan har nan da shekarar 2030 ba a samar da gagaruman sauyi kuma cikin gaggawa don tunkarar matsalar ba.

Shirin ya buƙaci zaftare yawan sinadaran Carbon ɗin da ƙasashe ke fitar wa da aƙalla ruɓanye 7 Matuƙar ana buqatar ceto Duniya daga halin da ta samu kanta a ciki.