Syria ke kan gaba wajen mutuwar mutane a sanadiyyar bam

Wani rahoto ya gano yadda Ƙasar Syria ke kan gaba a yawan mutanen da suka fi jigata ko kuma rasa rayukansu sanadiyyar bama-baman da ake binnewa a gefen hanyoyi lokacin yaƙi, wanda ke nuna cewa ƙasar ta sha gaban Afghanistan, wacce a bara ta zama jagora wajen fama da matsalar tashin bom.

Wani rahoton shekara shekara da hukumar kula da ababen fashewar ƙarƙashin ƙasa ta Duniya kan fitar tun daga 1999 ta ce, aƙalla mutane 2,729 ne ko dai suka rasa ransu ko kuma suka jikkata sanadiyyar ababen fashewar na ƙarƙashin ƙasa a Syria.

Daga shekarar 2005 zuwa 2007 dai Colombia ke matsayin mafi yawan waɗanda kan cutu daga ababen fashewar na ƙarƙashin ƙasa gabanin Afghanistan ta karɓe jagoranci fiye da shekaru 14 a jere in banda bara da Syria ta shige gaba.

Rahoton hukumar na bana ya nuna yadda mutum 2,492 suka mutu sakamakon taka ababen fashewar baya ga wasu mutum 7,73 da suka jikkata cikin ƙasashe 54.

Alƙaluman mutanen da suka cutu daga ababen fashewar na ƙarƙashin ƙasa a cewar rahoton ya yi ƙasa da wanda aka gani a shekarar 2016 na jumullar mutum 9,440 ko da ya ke ya kuma ɗara alƙaluman shekarar 2019 inda aka samu mutum 5,853 waɗanda ko dai suka jikkata ko kuma rasa rayukansu sanadiyyar ababen fashewar na ƙarƙashin ƙasa.

Rahoton ya ce har yanzu an gaza samun alƙaluma ƙasa da mutum 3,456 wanda aka samu a shekarar 2013 duk da yadda ƙasashe 164 suka shiga yarjejeniyar haramta dasa ababen fashewa a ƙarƙashin ƙasa tun shekarar 1997.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *