Mayaƙan ISWAP sun fara karɓar Zakka a Barno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Manoma da wasu mazauna garin Damboa da ke Jihar Barno sun fara bada Zakka ga mayaƙan ISWAP masu alaƙa da Boko Haram.

Zakka dai ɗaya ce daga cikin shika-shikan addinin Musulunci, kuma da ta zama wajibi ga wanda yake da hali ya fitar a duk shekara ga masu rauni da mabuƙata.

Wani babban jigo a cikin gwamnatin jihar Barno ya shaida wa wakilin Dailytrust cewa yawancin manoma suna zama ne a ƙarƙashin ikon mayaƙan ISWAP a yankin Damboa.

“‘Yan ta’adda sun yarda mutanen garin su yi noma, kuma suna karɓar zakka a duk shekara daga hannun kowane manomi bayan ya girbe amfanin gonar sa,” ya ce.

Majiyar ta ce, manoman ba sa son tsarin da mayaƙan ISWAP ɗin suka shigo da shi.

“Lokacin Boko Haram, a Shekau sun addabi wannan yanki, ba sa ko barin mutane suna zuwa gonakin su; da ISWAP ta zo kuma, sai suka ce mutane su je gonakin su, amma kuma dole ne su biya haraji da kuma fitar da zakka,” ya ce.

Wani manomi a yankin mai suna Musa Mrusha, ya bayyana cewa da yawa mutanen yankin ba sa so hukumomin gwamnati su san da haka.

“A baya da yawa mayaƙan Boko Haram sun kashe manoma da yawan gaske a lokacin da suke gyaran amfanin gonar su da kaka. Amma ka taɓa jin makamancin haka bana?

“Watan da ya gabata sun zo sun same ni a gonata suka ce min idan lokacin cire amfanin gona ya yi suna da kason su, wanda kuma na yarda na amince,” inji Musa.

Manhaja ta gano cewa mayaƙan ISWAP da suka yi ƙaurin suna wajen ta’addanci a Arewacin Jihar Barno, kwanan nan sun karkata da ta’addancin su zuwa kudancin jihar.

Ko a watannin da suka gabata mayaƙan sun soma karvar ‘kuɗin la’adar hanya’ wajen direbobi da kuma haraji a wajen manoma.

Wani fasinja mai suna Isma’il ya ce ‘yan ta’addan suna aiken direbobi da ke tafiya akan hanya domin su sayo masu wasu kayayyaki daga Biu lokacin da suke komawa.

“Suna da shingen dakatar da ababen hawa a Sabon Gari a yankin Yemantan da kuma ƙaramin shinge a Ruga. Suna kuma tsayawa ne wurin da suke iya hangen mota daga nesa sosai.

“Suna yin shiga kamar sojoji, wanda da zarar direba ya gan su zai tsaya,” inji Isma’il.