A cigaba da tattauna muhimman batutuwan da suka shafi watan Ramadan mai albarka, a wannan makon ina so ne mu waiwayi batun cin amanar waɗanda suka amince mana. Kuma kamar yadda muka sani cin amana babban laifi, ba kawai a cikin watan Ramadan ba, har ma a kowanne lokaci. Cin amanar wanda ya yarda da kai na cikin alamomin munafuki da addinin Musulunci ya zayyana. Zaman ka munafuki kuwa mummunar shaida ce a gareka, saboda hakan na nuni da cewa kai ba abin yarda ba ne, kuma ba mutum ne na ƙwarai ba!
A zamantakewar da muke ciki a ƙasar nan, cin amana ya zama ruwan dare, ba ga manya masu riƙe da madafun iko ba, har ma da na ƙasa, waɗanda ake jagoranta. Ta yadda hakan ya zama ana kallonsa ba a bakin komai ba. Har wasu na kallon cin amana a matsayin nema wa kai mafita. In ma an ga kai mai kiyaye gaskiya ne da tsare amana sai a riƙa kallonka a matsayin marar wayewa ko marar fahimtar inda rayuwa ta sa gaba. Har ma idan ba Allah ne ya kiyaye ba, sai ka ga wasu na ƙoƙarin kawar da mai gaskiya daga matsayin da yake, domin a kawo wanda zai riƙa ba da haɗin kai, ana yin ci-mu-ci. A ganinsu wannan ita ce kaɗai hanyar amfana da inuwar mulki ko samun romon dimukraɗiyya.
A makon da ya gabata mun ga rahotannin da suka nuna irin yadda Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bankaɗo wata almundahana da wasu muƙarrabansa suke yi wajen batun abincin buɗa-baki da gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin dafawa da rabawa talakawa da mabuƙata. Aikin da aka ƙiyasta zai ci kuɗi har Naira Biliyan ɗaya, kamar yadda gwamnatin jihar ta tabbatar, a maimakon Naira Biliyan 6 da Kwamishinan Watsa Labaran jihar ya faɗa tun da farko.
Sai dai duk da wannan zunzurutun kuɗi da gwamnatin ta ce ta ware domin ciyarwa da azumi, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna matuƙar ɓacin ransa da yadda ya tarar ana aikin abincin rabawa talakawa, inda ya bayyana cewa hakan ya saɓawa ƙa’idojin da aka gindaya wa jami’an gwamnati da aka ɗorawa alhakin gabatar da shirin.
Har ma an jiyo gwamnan yana kokawa kan cewa, duk wanda aka ɗauko aka bai wa amana ko babba ko ƙarami sai ya ci! Wannan abin yana ɗaga masa hankali matuƙa, har yana hana masa runtsawa.
Wannan ba shi ne karon farko da ake zargin wasu daga cikin waɗanda gwamnatin Jihar Kano ke bai wa alhakin gudanar da wani aikin al’umma suna nuna cin amana da almundahana ba, don ko a ƙarshen shekarar da ta gabata ma sai da Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta sanar da kama wani mai suna Tasi’u Al’amin-Roba, babban mataimaki na musamman (SSA), ga gwamnan jihar da kuma wani Abdulkadir Muhammad bisa zargin su da aka yi da laifin karkatar da kayan abincin tallafi da gwamnatin jihar ta bayar a rabawa talakawa Jihar Kano.
A cewar Kwamishinan ’yan sandan jihar Hussaini Gumel, an kama waɗanda ake zargin ne a wani ɗakin ajiyar kaya da ke Sharaɗa ɗauke da buhunan shinkafa da masara sama da 200, waɗanda suka karkatar da su daga cikin buhunan da aka ba su amanar rabawa jama’a.
Akwai ma wani rahoton da ya bayyana cewa Gwamnan kano Abba Kabir Yusuf na ya dakatar da Manajan Daraktan Kamfanin Samar da kayayyakin aikin gona na Kano (KASCO) Dakta Tukur Dayyabu Minjibir, bisa zarginsa da hannu a sayar da hatsi mallakin gwamnatin Jihar Kano.
Na kawo waɗannan misalai ne domin kafa hujja kan cewa, lallai ne Gwamnan Jihar Kano ya nuna matuƙar damuwa kan halin cin amana daga wasu muƙarraban gwamnati, waɗanda gwamnatinsa ta zaɓo su ta bai wa wannan amana, sakamakon amincewar da ta nuna musu. Akasarinsu ma ana yi musu kallon ’yan gani kashenin siyasar Kwankwasiyya ne, wacce takenta ma shi ne AMANA!
Wannan badaƙala da almundahana ba a gwamnatin Jihar Kano kawai ake samunta ba, kusan tun daga matakin gwamnatin tarayya har zuwa ƙananan hukumomi da ƙungiyoyin addini da na al’umma ana samun zarge-zarge da tabbaci ma kan wasu da suka ci amana ko suka yi yunƙurin cin amanar da aka basu, daga baya asirinsu ya tonu. Cin amana da rashin gaskiya na daga cikin munanan halayen mutane da ke jawo wa ƙasa koma-baya da taɓarɓarewar tattalin arziki, saboda yadda wasu ke jirkita tsarin da aka samar na cigaba da ƙoƙarin samar da gyara.
Babban saƙon da rubutuna na wannan mako yake ƙoƙarin isarwa shi ne, cin amanar da wasu da ke kiran kansu da Musulmi suke yi a cikin wannan wata mai alfarma. Duk kuwa da yadda ta bayyana ƙarara cewa mutane da dama na rayuwa cikin ƙunci da rashin sanin yaya za su yi su samu abincin buɗa-baki, saboda talauci da yake addabar ƙasa. Amma sai ka ga wasu sun rufe ido sun kantara rashin gaskiya da amana, wajen rabon kayan abinci da ake basu, don isarwa ga jama’a ko ƙungiyoyin tallafawa mabuƙata.
Hajiya Farida Shehu, ita ce shugabar ƙungiyar tallafawa marayu da zawarawa mai suna Alheri Danƙo Ne Charity Foundation, ta samu kira daga wajen wani bawan Allah da ya bai wa ƙungiyar gudunmawar buhunan shinkafa 20 domin a rabawa jama’a mabuƙata. Amma abin da zai baka mamaki bayan sun tattauna da mutumin nan kan ga yadda kayan abincin nan zai isa gareta, sai ga kira daga wajen wani na hannun daman wannan bawan Allah yana sanar mata da cewa saƙonta na buhun shinkafa 5 yana wajensa. Alhalin buhu 20 shi wanda ya ba da tallafin ya ce a bayar. Cikin awoyi kaɗan har ya zabtare buhu 15 shi kaɗai, duk kuwa da kasancewar amana aka ba shi ya isar saboda an yarda da shi.
Kodayake daga baya dai ƙungiyar Alheri Danƙo Ne ta samu saƙonta cikakke yadda tunda farko aka kira aka sanar da ita. Amma saƙon da nake ƙoƙarin isarwa a nan shi ne yadda amana ta yi ƙaranci a zukatan jama’a. Tun daga masu kusanci da addini har zuwa ’yan siyasa da muƙarrabansu. Musamman ma a cikin watan Ramadan, inda lokaci ne da ake son muminai su shagaltu da ayyukan neman lada, da neman kuɓuta daga wuta, amma sai a samu wasu baragurbi suna nuna maitarsu a fili, saboda rashin tsoron Allah, suna ha’intar waɗanda suka yarda da su.
Ina mai jan hankalin ’yan uwa musulmi da sauran jama’a mu gane cewa, bai kamata mu riƙa bari son zuciyarmu yana jefa mu cikin fushin Allah ba. Har ma kuma ya jawo mana asarar ɗimbin ladan da ake garaɓasarsa a cikin wannan wata mai ɗimbin albarka. Sannan ga shugabanni, lallai su riƙa tantancewa da bibiyar ayyukan da suke ɗora muƙarrabansu a kai, domin kuwa wasu daga ciki ba tsakani da Allah suke zaune da su ba, kuma ba abin yarda ba ne.
Duk mutumin da za a bai wa amana saboda an yarda da shi, amma son zuciya ya sa ya ci wannan amana to, babu shakka wannan mutumin abin tsoro ne. Irinsu ne ake haɗa baki da su a cutar da wanda ke tare da su, ko iyalinsa, saboda ba su da gaskiya da amana.
Ya Allah Ka sa mu fi ƙarfin zukatanmu, ka nisantamu daga cin amanar waɗanda suka yarda da mu. Amin
