
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Lantarki, Cif Adebayo Adelabu ya tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana aiki tuƙuru wajen ganin an samu wadatar wutar lantarki gabannin ƙarewar wa’adinsa a shekarar 2027.
Da ya ke magana a ranar Lahadi yayin ƙaddamar da tashar lantarkin yankin Kwaru mai ƙarfin 1X15MVA 33/11KV a Ikotun-Egbe da ke Jihar Legas, Adelabu ya ce an samu gagarumar nasara a shirin Sabunta Fata na shugaban ƙasa ɓangaren samar da lantarki.
Ya bayyana hakan a matsayin abinda ka iya kawo ƙarshen matsalolin rashin samun isashshen lantarki acikin al’ummar Nijeriya.
Ya ce, Gwamnatin Tarayya tana bin hanyoyin da suka dace wajen magance matsalar isarwa da raba lantarki a sassan ƙasar, yana mai cewa ba lallai a cika dukkan alƙawuran da aka ɗauka ba zuwa 2027 saidai suna fatan cimma hakan a lokacin.
A shekarar 2023 yayin yaƙin neman zaɓe, Shugaba Tinubu ya yi alƙawarin shawo kan matsalolin lantarki a Nijeriya cikin shekaru huɗu, lamarin da ya haddasa cecekuce a ƴan kwanakin na duba da yadda wa’adin mulkin nasa ya wuce tsakiya ba a daina samun tsaiko a fannin ba.
Adelabu ya ƙara da cewa, sabuwar tashar za ta taimaka wajen haɓaka raba wuta a wasu yankunan Legas da kewayenta, lamarin da a cewarsa zai bunƙasa harkar ƙananan ƴan kasuwa da tattalinsu.
