Borno: Kada ku tada hankali, mu na kula da yanayin – Gwamna Zulum kan barazanar ambaliya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kirayi al’ummar jihar da su kwantar da hankali yayin da matakin ruwa a madatsar Alau ke ƙara yawa, yana mai tabbatar wa ƴan Maiduguri cews suna aikin kula da al’amarin wajen ɗaukar matakan da suka dace don kauce wa aukuwar ambaliya.

Zulum ya bayyana haka ne yayin da mazauna yankunan da ke fuskantar barazanar aukuwar ambaliya suka koka sakamakon samun ruwan sama akai-akai da ake samu a ƴan kwanakin nan, lamarin da ka iya haddasa ambaliya.

Da ya ke magana yayin ziyarar gani da ido kan aikin sake gina wani sashi na madatsar Alau, Farfesa Zulum ya ce suna sane da halin da al’ummar ke ciki na fargaba, wanda a cewarsa gwamnati na iya ƙoƙarinta waje ganin ta kauce wa faruwar iftila’in.

Ya ce, tuni aka gina wasu magudanan ruwa domin rage wa Alua ƙarfi ta yadda ruwan cikinsa ba zai yi yawan da zai fasa wani sashi ba kamar yadda ya faru a shekarar da ta gabata.

Ya bayyana cewa, akwai buƙatar nazari akai-akai da zama a ankare ga hukumomin da lamarin ya rataya a wuyansu, yana mai jinjina wa injiniyoyin da ke aiki akan lamarin.

Kazalika, ya yi kira ga al’umma da su bai wa hukumomin haɗin kai wajen kula da wuraren da suke zubar da shara da tsara gine-gine a birane.

By Babaji