
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun Atisayen Whirl Stroke na rundunar sojoji Nijeriya da ke Birget ta 6 da haɗin-gwiwar jami’an Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS), sun yi nasarar ceto Injiniya Joshua Saleh, wanda lakcara ne a Jami’ar Taraba.
Blueprint ta ruwaito cewa wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da malamin a ranar 31 ga Yuli a hanyar Chinlai zuwa Kente zuwa Wukari da ke Ƙaramar Hukumar Wukari a Jihar Taraba.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ta 6, Laftanal Umar Muhammad ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ƙarshen mako.
Ya ce, dakarun sun yi aikin ceto malamin ne a lokacin da suka samu bayanan sirri game da maɓoyar ƴan bindigar, lamarin da ya sa suka kutsa lungu da saƙo domin kai wa gare su.
A lokacin da suka riske su, sojojin sun yi musayar wuta da su, lamarin da sa ƴan bindigar suka tsere a lokacin da ta tabbata an fi ƙarfinsu.
Da ya ke jinjina wa ƙoƙarin dakarun, Kwamandan rundunar Birgediya Janar Kingsley Chidiebere ya yaba wa hoɓɓasa da suka yi tare da haɗin-gwiwar sauran hukumomin tsaron.
Ya kuma tabbatar wa al’umma za su cigaba da ƙoƙarin bai wa rayuka da dukiyoyinsu tsaro a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
Haka kuma ya kiraye su da cigaba da sanya ido da bai wa dakarun haɗin kai a ƙoƙarinsu da daƙile ayyukan ta’addanci a cikin al’umma.
