Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Sannunku da jimirin bibiyar jaridar Blueprint Manhaja.
A makon baya, mun fara kawo maku bayanai kan amfanin darbejiya ga fata. Inda kuma sanar da ku cewa, wannan sati za mu cigaba.
Kamar yadda muke faɗa tun a farkon darasin, iccen darbejiya ba sabon abu ba ne ga magungunan gargajiya. Amma yanzu, masana kimiyyar kula da fata sun tabbatar da amfaninsa cikin sahihancin bincike. A yau, yawancin cream, soap, da face wash na zamani suna ɗauke da sinadaran darbejiya saboda ƙarfinsa wajen gyara da kare fata.
3. Sabunta sabuwar fata (Eɗfoliation):
Darbejiya tana taimaka wa wajen cire tsohor fata, ta bar sabuwar fata mai laushi da sheƙi. Fatar da ake wankewa da garin ganyen darbejiya tana saurin rabuwa da matatar fata, wanda hakan na nufin zata yi taushi kamar fatar yara
Hanyar amfani:
A niƙe ganyen darbejiya busasshe, a gauraya da ‘yar madara ko yogurt. A shafa a jiki a matsayin body scrub a lokacin wanka. Zaki lura da bambanci tun bayan mako guda.
4. Kare fata daga rana da tsufan wuri:
Sinadaran antioɗidant da ke cikin darbejiya suna kare fata daga lalacewar da rana ke haifarwa da kuma tsufar da ke zuwa da wuri. Idan ana shan ƙura ko rana mai zafi, amfani da darbejiya na kare fata daga ƙonewa da duhu.
Hanyar amfani:
A haɗa neem oil da ɗan shea butter ko man zaitun, a shafa kafin fita rana. Yana kare fata kamar natural sunscreen.
5. Fatar kai da gashi:
Ba fata kawai ba, darbejiya na da amfani wajen magance ƙurajen kai, dandruff da kuma ƙarfafa gashi. Idan ana wanke kai da ruwan darbejiya, yana kawar da kaikayi da ƙurajen kai, kuma yana sa gashi ya yi ƙarfi ba tare da zubewa ba.
Daga ƙarshe mu sani, ƙyakkyawar fata ba ta tsaya a iya amfani da magunguna masu tsada ba, domin takan samu da tsafta, da amfani da albarkatun da suke zagaye da mu.
Darbejiya kawai na iya zama amintacciyar abokiyar mace, mai kare fata, mai gyaranta, kuma mai ɗaukaka kwalliyarta cikin salo dawamame ba jeka ka dawo ba.
