Muhimman hanyoyi 10 na kula da fata (2)

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a wannan shafi na Kwalliya. Sannunku da jimirin bibiyar mu.

A ci gaba da tattaunawa kan muhimman hanyoyin kula da fata, idan mai karatu bai manta ba, mun kawo guda biyu a makon da ya gabata, bayan mun yi shimfiɗa kan abinda ake nufi da kula da fata.

3. Amfani da man kare fata daga rana:

Rana na ɗaya daga cikin ababen da ke yi wa fata lahani, idan na ce rana ina nufin ranar da zata fito sosai, kamar daga sha ɗaya na safe zuwa sama. Domin a cewar masana rana wadda ta fito a farkon safiya na da amfani ga fata, hakan na nufin tun daga hudowar ranar zuwa fara kaifin ta, tsakanin bakwai na safe zuwa tara, idan kuwa lokutan tsananin zafi ne ba za ta kai hakan ba.

Abin nufi dai anan muna magana ne kan rana idan ta yi zafi. Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da wasu ke kasa gane fatarsu, duk da cewa suna kashe kuɗaɗe wurin siyen kayan gyaranta.

Idan mun lura, macen da ba ta fiye fita ba da wadda kuwa kullum sai ta fita fatarsu na da banbamci ta fuskar lafiya, musamman a lokutan zafi.

Don haka yin amfani da mayukan kare fata daga rana, wato abinda bature ya kira da ‘sunscreen’ masu bada kariya ta gaba ɗaya SPF 30 ko fiye hanya ce ta hana rana tasiri a fata musamman a lokuta na zafi, kai har lokutan da ranar ba ta fito sosai ba.

Wasu masana fata na ganin ba wa fata kariya daga rana na ɗaya daga cikin rigakafin kamuwa da cutar tsufa da wuri ko ma sankarar fata.

4. Cin abinci mai gina jiki:

Zancen cin abinci mai gina jiki don gyara fata kuwa shafin Kwalliya ba a yau zai fara faɗa ba, kusan mun faɗa, mun sake faɗa, don haka tuni kawai za mu ƙara yi. Abinci mai inganci ne ƙashin bayan duk wani ci gaban da fata za ta samu.

Cin abinci mai ɗauke da antioɗidants kamar ‘ya’yan itatuwa da sauran kayan lambu, kamar kabeji da sauransu. Sannan a rage yawan sukari da abinci mai yawan matsƙi.

Za mu ci gaba mako mai zuwa.

By ukarofi