Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Bayar da Bashin Karatu ta Nijeriya (NELFUND) ta ce ta ba ɗaliban Nijeriya rancen kuɗi Naira Biliyan 56.55 domin biyan kuɗin makaranta da alawus ɗin kashewa na yau da kullum.
Hukumar ta bayyana haka ne domin bayyana nasarorin da ta samu a cikin shekara ɗaya da fara aiki tun bayan ƙirƙirar shirin.
A wata sanarwa da daraktan sadarwa na hukumar, Oseyemi Oluwatuyi ta fitar, ya ce sama da ɗalibai 600,000 ne suke neman rancen.
“Bayan tantancewa, mun amince tare da ba ɗalibai 550,000 rancen, inda muka ba su kuɗi naira biliyan 56.85 a cikin shekara guda.”
“Tsarin bayar da rancen ya taimaka wajen sauƙaƙa wa ɗaliban Nijeriya da iyaye,” inji ta.
“A cikin watanni goma sha biyu kacal, NELFUND ta canja hanyar samun tallafin ilimi tare da sama da ɗalibai 600,000 da suka yi rajista, sama da 550,000 sun samu nasarar neman lamuni da N56.85 biliyan domin biyan kuɗin makaranta da kuma samar da alawus-alawus.
“Wannan nasarar ta nuna ikon da manufa mai ma’ana da ke goyon bayan aiwatar da shirin. Shirin rancen ɗalibai na NELFUND ya kawo sauƙi ga iyalai, ya maido da fata ga ɗalibai, kuma ya samar da hanyar samun nasarar ilimi da sana’a a faɗin Nijeriya.
“Ta hanyar ci gaba da hacin gwiwa tare da cibiyoyi, gwamnatocin jihohi, da ƙungiyoyin ɗalibai, asusun ya ci gaba da jajircewa wajen zurfafa ayyukan sa inganta rancen ɗalibai.
“Kamar yadda NELFUND ke duban gaba, ta tsaya tsayin daka kan manufarta na tabbatar da cewa babu wani ɗalibin Nijeriya da aka hana karatu saboda ƙarancin kuɗi.”
Da yake jawabi, Manajan Daraktan NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr, ya ce asusun wata gada ce ga dama, daidaito da kuma sauyin ƙasa.
“Shekara ɗaya da ta wuce, mun ƙaddamar da alƙawari ga ɗaliban Nijeriya, a yau, muna alfahari da cika wannan alƙawari, NELFUND ya wuce tsarin lamuni, wata gada ce ta dama, daidaito, da kuma kawo sauyi a ƙasa,” inji shi.
