Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta ce za yi wa ’yan Nijeriya gwanjon rukunin gidaje da ta ƙwace a Abuja a hannun tsohon Gwamnan Babban Bankin ƙasar, Godwin Emefiele.
Bayanin haka ya fito ne lokacin da Ministan Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane Ahmed Dangiwa da kuma shugaban hukumar EFCC Olanipekun Olukoyede, suka jagoranci wata tawaga zuwa rukunin gidajen da aka ƙwace.
EFCC ce ta, ƙwace gidajen waɗanda ke alaƙa da Emefiele a watan Disamban 2024, inda aka miƙa su ga ma’aikatar bayan umarni da shugaba Tinubu ya bayar.
Lokacin ziyarar gani da idon, Dangiwa ya sanar da cewa ma’aikatar za ta fara aikin duba ingancin gidajen.
Ya ce, bayan kammala duba su, za a samar da wani shafi wanda ‘yan Nijeriya za su shiga su nemi damar saya.
Ministan ya ƙara nanata zimmar gwamnatin tarayya wajen yin komai bisa gaskiya da adalci, inda ya yi kira ga jami’an gwamnati da su guji shiga abubuwan da ba su dace ba.
Dangane da yanayin siyar, ya ce za a yi amfani da tashar tashar ma’aikatar, yana mai yin alƙawarin cewa zaɓukan biyan kuɗi za su kasance masu sassauƙa.
Ya ce, “Gidajen da ma’aikatar ta sayar za su kasance suna da sassauƙan zaɓuɓɓukan biyan kuɗi, da suka haɗa da jinginar gida, ƙayyadewa, biyan hayar gida, da dai sauransu, walau a irin wannan yanayi ko kuma wani.
“Waɗannan guda 753 ne kacal.
“Ma’aikatar tana da tashar yanar gizo da aka haɓaka inda ake sayar da waɗannan gidaje – renewedhopehomes.fmhud.gov.ng. Ministan ya riga ya bayyana cewa za a yi amfani da irin wannan tsari wajen sayar da waɗannan gidajen da aka ƙwace.”
Da aka tambaye shi game da ranar da za a buɗe tashar ga ‘yan Nijeriya masu sha’awa, sai ya ce, “Ma’aikatar gidaje ba ta riga ta kammala dukkan shirye-shirye ba.”
Ya yi watsi da raɗe-raɗin cewa za a raba gidajen ga masu riƙe da madafun iko.
Haiba ta ce, “A ko da yaushe mutane za su yi hasashe, wataƙila saboda abubuwan da suka faru a shekarun baya, gwamnatin Shugaba Tinubu na yanzu tana yin wani abu na daban wajen inganta gaskiya da riƙon amana.
“Ba zan iya gaya muku abin da ma’aikatar ke yi ba, tare da sabunta shafin hopehomes.fmhud.goɓ.ng, ma’aikatar ta katse tsoma bakin mutane don tabbatar da cewa tsarin ya kasance a bayyane kuma ya haɗa da kowa.
“Kowane ɗan Nijeriya zai iya samun gidan, inda zai shiga tashar yanar gizon, ya bincika nau’ikan gida da wurare daban-daban, ya zaɓi gidan da yake so, zaɓi biyan kuɗi, gabatar da wasu abubuwa, sannan ya sami takardar izini nan da nan.”
