Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Manyan ‘yan siyasar Nijeriya da ke jagorantar shirin yin haɗaka tsakanin jam’iyyun hamayya domin tunkarar APC a zaɓen 2027, sun mayarwa ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP martani, a kan matsayar da gwamnonin suka ɗauka cewa ba su goyon bayan ƙulla duk wata haɗaka da za ta fitar da su daga PDP.
Gamayyar ‘yan adawar da ta haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023 da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai da dai sauran ‘yan siyasa, ta ce nan ba da jimawa ba za a sanar da ƙulla sabuwar haɗakar siyasa da za ta ceto Nijeriya daga mulkin APC.
ɗaya daga cikin jagororin tafiyar ƙulla sabuwar haɗakar siyasar ta Nijeriya kuma tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa mai kula da shiyyar Arewa Maso Yamma, Salihu Lukman ya yi zargin cewa gwamnonin PDPn na sane cewa jam’iyyar su ta yi lalacewar da gyaran ta zai yi wahalar gaske, domin haka suke neman tallafawa jam’iyyar APC mai mulki da zummar ganin ‘yan adawa ba su yi nasarar gabatar da ɗan takara mai nagarta ba a zaɓen 2027.
A ranar 20 ga watan Maris Alhaji Atiku Abubakar da Peter Obi da kuma magoya baya su suka sanar da shirinsu na ƙulla wata gamayyar siyasa da za ta tunkari APC a zaɓen 2027 mai zuwa.
Sanarwar ta su ta janyo muhawara da tsokaci daga ɓangarori daban-daban.
Sai dai a ƙarshen wani taron da suka yi a ranar Litinin 15 ga watan Afirilu a garin Ibadan, gwamnonin jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad sun yi watsi da yunƙurin kafa gamayyar suna jaddada cewa jam’iyyar suba za ta narke cikin wata gamayya ta daban ba.
A hirar sa da BBC, Malam Salihu Lukman ya gargaɗi gwamnonin na PDP da su sani cewa matakin na su wani yunƙuri ne na son ganin an tsayar da ɗan takara mara ƙarfi, don taimaka wa Shugaba Tinubu na Jam’iyyar APC wajen samun nasara a zaɓen mai zuwa.
Ya yi bayanin cewa a halin da Nijeriya ke ciki yanzu, lokaci ne da ‘yan siyasa za su taru waje guda ”Mu cire son zuciya, mu fahimci halin da ƙasar nan ke ciki, dole ne mu daure kowa ya zo a yi abin da ya kamata.’
”Ba daidai ba ne a ƙasa kamar Nijeriya a ce baya ga jam’iyyar da take riƙe da gwamnati mai ci, duk sauran jam’iyyun sun shiga halin ƙaƙa nikayi, a zauna ana kallo har a kai gaɓar da za a yi zaɓe kuma a gaza tsayar da ‘yan takara” inji Salihu Lukman.
Ya ƙara da cewa abin da ya janyo tafiyar ta su ta neman kafa gangamin kenan kuma suna fatan cikin gwamnonin PDPn za a samu masu fahimta da za su shiga domin a yi tafiyar tare da su.
Dangane da dalilin da gwamnonin PDP suka bayar cewa su ba za su fita daga jam’iyyar su domin komawa cikin wata jam’iyya da ko kansila ba ta da shi kuwa, Malam Salihu Lukman ya ce ”Na farko tambayar ita ce ina jam’iyyar PDP take, ta taɓa ganin jam’iyyar da ta yi shekara biyu ta kasa yin meeting? A yanzu a halin da PDP da Labour party da NNPP suke, dukka suna cikin hatsarin da ba za su iya tsayar da ‘yan takara ba.”
Ya tabbatar da cewa a ɓangaren su, shiri ya kusan kammaluwa kuma nan ba da jimawa ba za su sanar da kafa wata sabuwar haɗakar siyasa da za ta ƙumshi duk wani ɗan siyasa ”mai kishin ƙasa wanda yake son ganin Nijeriya ta gyaru domin kafa jam’iyyar da za ta tsaya da ƙafafunta domin tsayar da ‘yan takara masu nagarta”.
Masu sharhi dai na ci gaba da bayar da ra’ayoyi mabanbanta game da tasiri ko akasin haka da wannan sabuwar haɗaka ta ‘yan adawa za ta iya yi a babban zaɓen Nijeriya na 2027.
