Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) ya sanar da samun ribar Naira Tiriliyan 3.297 a shekarar da ta gataba, wanda hakan ya nuna ƙaruwar kashi 28 daga ribar Naira Tiriliyan 2.548 da aka samu a shekarar 2022.
Sanarwar da Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin, Olufemi Soneye, ya fitar a ranar Litinin ya bayyana cewa, wannan nasarar da aka samu, wadda ita ce mafi girma a tarihin kamfanin na tsawon shekaru 46, an bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai na duniya da aka gudanar a ginin NNPC da ke Abuja.
Sanarwar ta ce, “Kamfanin NNPC ya fitar da bayaninsa na filla-filla kan ‘Audited Financial Statement’ (AFS) na shekarar 2023, inda ya bayyana ribar Naira tiriliyan 3.297 a ƙarshen shekarar da ta ƙare a watan Disamba 2023, ƙarin sama da Naira Biliyan 700b (kashi 28) idan aka kwatanta da ribar 2022 na Naira tiriliyan 2.548.”
Da yake jawabi a wajen taron, babban jami’in kula da harkokin kuɗi na kamfanin NNPC, Umar Ajiya, ya bayyana muhimmancin gudanar da ayyukan kasafin kuɗin kamfanin, inda ya danganta hakan ga hangen nesa da kuma juriya na aiki.”
Ya nanata cewa fitar da bayanan Audited Financial Statement (AFS) ya jaddada ƙudirin NNPC na yin gaskiya da riƙon amana.
“Ayyukan mu na kasafin kuɗi yana nuna hangen nesa na dabaru da juriya na aiki. Duk da ƙalubalen da ke tattare da yanayin ayyukanmu da tattalin arzikinmu, mun inganta ayyukan wannan babban kamfani da kuma ayyukan kuɗi,” inji Ajiya.
